
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da tallafi saboda matsin rayuwa tare da rage wasu kuɗaɗen haraji ga ma’aikata domin rage raɗaɗin hauhawar farashin fetur.
NLC ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen sauƙaƙa wa ma’aikata game da matsin tattalin arzikin da ya biyo bayan hauhawar farashin man fetur a Nijeriya.
Ƙungiyar ta ce tashin farashin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke shafar kasuwannin makamashi na duniya.
A cewar NLC, idan gwamnati ta samar da irin wannan tallafi da rage haraji, hakan zai taimaka wa ma’aikata tare da rage tasirin hauhawar farashi ga iyalansu.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar NLC tana ganin matakin zai zama ɗaya daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen tallafa wa ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu yayin da suke cikin halin matsin.
