Sabbin darussa 70 sun samu amincewa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli

Spread the love

Gyare-gyaren da gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani ke aiwatarwa a ɓangaren ilimi na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau, inda  Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ta samu gagarumin ci gaba a fannin tantance darussa, gina ababen more rayuwa da kuma kula da jin daɗin ɗalibai.

Shugaban kwalejin  Injiniya Muhammad Kabir Abdullah, ne ya bayyana haka yayin da yake karɓar tawagar ‘yan jarida a rangadin da suka kai harabar makarantar da ke Zariya.

Ya ce goyon bayan da gwamnatin jihar ke bayarwa ya taimaka matuƙa wajen samun amincewar sabbin shirye-shiryen karatu daga hukumomin kula da ilimin fasaha wato NBTE da kuma NCCE.

Sabbin darussan da aka samu amincewar koyarwa sun haɗa da  babbar Difiloma akan ilimi  da fasahar kimiyyar zamani da fannin  Shari’a  da dai  sauran su. 
Hakan ya sa adadin darussan da kwalejin ke koyarwa da suka samu cikakkiyar amincewa ya kai kusan 70.

Injiniya Abdullah ya bayyana cewa tun bayan hawan Uba Sani kan mulki, makarantar ta samu gagarumin ci gaba a ɓangarorin kuɗaɗen gudanarwa, faɗaɗa shirye-shiryen karatu, ɗaukar sabbin ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba, da kuma inganta gine-ginen makaranta, wanda ya nuna ƙudirin gwamnati na ƙarfafa ilimin fasaha da na sana’o’i.

A nasa jawabin yayin rangadin, Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce zuba jari da gwamnati ke yi a fannin ilimi na daga cikin manyan manufofin gyaran da gwamnatin Uba Sani ke aiwatarwa domin inganta ilimi da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya ce manufar ita ce horar da ɗalibai da ƙwarewar da kasuwar aiki ke buƙata, domin rage rashin aikin yi da kuma magance matsalolin tashin hankali da rashin tsaro a jihar.
Shi ma shugaban ƙungiyar ɗalibai (SUG) na makarantar, Abubakar Buhari, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa matakan da ta ɗauka na inganta jin daɗin ɗalibai, musamman gyaran ɗakunan kwanan ɗalibai da kuma rage kuɗin makaranta da kashi 50 cikin 100 a duk manyan makarantu mallakin gwamnati a jihar.
Ya ce matakin ya kawo sauƙi ga ɗalibai da iyayensu, tare da ƙara buɗe damar samun ilimi ga matasa da inganta yanayin rayuwar ɗalibai a makarantar.

By ukarofi