Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ba haka kawai na ke wannan rubutun ba sai da hujjoji kwarara kamar hasken rana da ƙarfe 12 pm. ‘Yan kwangilar tada fitinar addini da ƙabilanci da amfani da rigar bagaye ta Hausawa ba Hausawa ba ne sam. Duk wanda ya san Arewa da gaske zai amince ba wani abu mai kama da wai Bahaushe ya mulki kansa! Neman tada fitina ne kawai don kwangila, tun da a hakika Arewa 100% na hannun Hausawa da masu amfani da harshen Hausa a matsayin harshensu na farko a rayuwa. Wautar ‘yan kwangilar ita ce sun dauka da zarar sun jefo sharrin a na nunawa Hausawa wariya har ma wai ’yan ta’adda Hausawa kaɗai su ke kashewa, shikenan sai a wayi gari misali daga tsakiyar Kano a shiga yaƙin ƙabilanci. Yo in ba shirme ba waye zai yaƙi ɗan uwansa? Haka Allah ya hukunta zaman al’ummar tare da ƙulla zumunci ta dukkan ɓangarorin alheri na rayuwa.
Waye Bahaushe waye Bafulatani a Kano, Waye Bahaushe waye Bafulatani a Katsina, Zazzau, Zamfara, Sokoto, Kebbi da sauran sassa? Makiran nan ba su san Hausawa su ke yaƙa da sunan Hausawa ba. In ba sakarci ba ka cewa Bahaushe wanda mahaifiyarsa ta ke Bafulatana ya kashe ta don ita dangin Bello Turji ce? Wa ma zai tabbatar Turji Bafulatani ne 100%. Ka cewa mutumin da mahaifinsa Bafulatani mahaifiyarsa Bahaushiya ce ya zabgawa mahaifinsa mari ko ya murɗe ma sa wuya don hakan shi ne hanyar yaki da ta’addanci? Duk wannan misali na tabbatar da ‘yan ta’adda ba su da wata alaƙa da wata ƙabila in ba a kwangilar ‘yan bazata ba masu samun ɗaurin gindi daga ma’abota addininan da ke aiki da son zuciya da kuma zugar ‘yan awaren IPOB.
Haƙiƙa da mutanen nan Hausawa ne kuma masu riƙo da addini, tabbas za su gane sun ɗauko maliya da ya sa a wannan kwangilar don ba wani Bahaushe ko Bafulatani musulmi ko ma Kanuri ko duk Musulmin Arewa da zai jingine addini ya shiga kisa don ƙabilanci, face in dama ɗan ta’adda ne mai wakiltar mugun aikinsa na ta’addanci. Duk wakokin Gambu mijin Kulu na ɓarayi bai taɓa alaƙanta sata ko ta’addanci da wata ƙabila ba sai ga aikin mai zarmiya.
Gabanin fara wannan kamfen na soshiyal midiya na iƙirarin Hausa zalla, duk masu dinka rigar bagayen nan da ƙirƙirar sunayen Bahaushe waye-waye ko ma su surka da Larabci Al-waye Hausawi kaza-kaza, duk ba sa marmarin harshen Hausa don hasalima sun fi son kwarewa da magana da Turanci don a ɗauka sun waye. In ka ga sun ɗan taɓuka a Hausa ko tarihin son kai sun hau manhajar CHATGPT ne da dakikai ke amfani da ita wajen fassara da rubutun sakarci na murɗe wuyan tarihi. Gaskiyar magana kwangilar nan na wahalar da miyagun nan don ba su san komai game da tarihi da al’adun Hausawa da ƙarfin imani da tauhidi na Hausawan ba, don haka sai ka ga mutum ko suturar Hausawa bai iya sakawa ba sai ‘yar sharar nan LAGOS JAMPA. In ka bar masu farafagandar nan har sarka za su kwama a wuya don a ɗauka sun waye. Kwanan nan haka su ka tsara hular Hana-Sallah da ‘yar digil din rigar Bature wai Hausa Zalla!. A ra’ayina Hausawa da al’ummar Arewa na daga cikin al’ummar duniya mafi more tufafi na fitar kunya.
A gurguje, na ga ‘yan bazata na yayata wasu hotunan da alamu na ARTIFICIAL INTELLIGENCE ne da ke nuna wasu maza da mata sanye da sutura ta fitsara wai Hausawa ne ke atisaye don motsa jiki. Akwai ma a hotunan inda wani ɗan bazata ya ɗora hannunsa kan kafaɗar wata mata mai damammun kaya da gashin doki a kanta wai duk Hausawa kenan. A ƙasar Hausa kakaf ba inda hakan ya taba faruwa sai a na’urorin wayoyin salula na ‘yan bazata da ke iƙirarin Hausa zalla ko. Na duba da zarar wani ya ja hankalin ‘yan bazata cewa shigar ba ta Hausawa ba ce sai ‘yan bazata su ba da amsa da saka hoton irin matan Fulanin nan na ruga masu tallar nono a garuruwa sanye da irin tufafin jahiliyya da ba ya rufe jiki yadda ya dace. Wannan na nuna ba da hujjar hotunan can na baɗalar Hausawan karya da na matan Fulanin daji masu tallar nono. Da mutanen nan sun san Musulunci, ko kuma ba Musulunci su ke yi wa zagon ƙasa ba, ba za su kare tsiraici da tsiraici ko fasiƙanci da fasiƙanci ko shirita da shiririta ba.
Kama daga al’adar wasu Yarbawa na zama mata da miji kafin aure WA JOKO ko Daduro da wasu ‘yan Arewa ke yi wato mutum ya ajiye wata mata kamar matarsa ba tare da aure ba, ko tallar nono da suturar da ke nuna tsiraici duk sun sabawa koyarwar musulunci da ma kyawawan al’adun Hausawa da Fulani da ma mutan kirki a Arewa. A fili fa don logar yayata wannan kamfen na yakin ƙabilanci, ‘yan bazata kan kore addini a rayuwarsu kuma hatta addinin Kiristancin; su na cewa ai batun ƙabila su ke yi ba addini ba, kuma kabila ta fi addini don kabila jini ce addini kuma imani ne, su kuma ba su da imani!. Wallahi miyagun nan ‘yan bazata ba sa bin koyarwar Alkur’ani kazalika ba sa bin koyawar BIBLE kawai ‘yan ta more ne maƙiya Hausawa da addinin Musulunci. Magabatansu ne, Shehu Mujaddadi ya yi ta fama da su don su rage fitsara.
Hanya mai sauƙi da za ka fahimci ‘yan bazata sun fito ne daga kananan ƙabilun ita ce ambatar Fulani da AGWAI wacce ‘yan Arewa ta tsakiya MIDIBELAWA ke yi amma Hausawa Fulani su ke ambata ko Hausar Katsina da ke cewa HILANI don ƙarin harshensu kamar KIFI sai su ce KIHI kamar LAFIYA sai su ce LAHIYA da sauran su. Su kan yi yarfe da zayyana Fulani haka kawai da ribar tallar nono da kuma tabbas sun san shafawa wata ƙabila bakin fenti ne da kullawa manyan malamai kazafi da neman zubar mu su mutunci don tsananin kiyayya. Shin in Agwai da su ke cewa ribar tallar nono ne, wa ke sayan nonon? Idan su na nufin a na samun ‘ya’ya shegu a tallar nono, su waye iyayen shegun? Gaskiyar magana Musulunci ya haramta wannan muguwar dabi’a ta yayata sharri da kalaman fasikanci. Ba Musulmin kirki da zai faɗi wannan kuma ba Kiristan kirki da zai fadi haka sai dai a kwangilar ‘yan bazata waɗanda su ka duƙufa dare da rana wajen kunna fitinar ƙabilanci a Arewa.
Shaharerren labari
A nan Arewa an samu wata babbar masarauta inda karuwai su ka cika masarautar a na ayyukan baɗala. Mutan gari su ka nuna damuwa kan haka. Hakan ya sa jama’a tinkarar mai martaba Sarki su ka bayyana ma sa wannan ƙorafin da buƙatar lallai a kori karuwai daga masarautar. Mutanen nan sun sha mamaki don maimakon mai martaba ya tada dogarai su yi kaca-kaca da karuwan, sai ya ce ba za a tashe su daga ƙasarsa ba! A takaice ko menene dalilin matsayar ta mai martaba? Yauwa cewa ya yi “in mutanen garin ba sa neman karuwai to ba yadda za a yi karuwai su zauna a garin!” don haka mutane su daina neman karuwai sai gari ya tsarkaka daga baɗala. Shin karuwai ne masu laifi ko mutan gari da ke neman karuwai?. Alamu na nuna in karuwan su ka bar garin ko a ka kore su daga masarautar, to duk inda su ka koma can zai zama mafi girman masarauta don mutane za su bi su amma nan don iya yi sun ce a kore maimakon su yi istigfari su tuba su gyara ɗabi’unsu.
Kammalawa
Shawara ta ga ‘yan bazata, su daina shigar burtu ga addinin musulunci, Tun da hoton Hausawa a wajensu shi ne mutane masu hana sallah da sutura damamma mai nuna tsiraici, su fito fili su yi harkarsu kar su batawa Hausawa suna kar kuma su fake da a na kafirtasu. Ba mai kafirta kowa don ai ba amfanin kafurta kowa sai dai aikin mutum ya kai shi ga wannan matsayin. Ina ribar aikin Baban-giwa, ina amfanin baɗi ba rai, ina ranar shuka a idon makwarwa? Kai kowa ya yi addininsa kuma ‘yan bazata su canja salo don na ga rashin hakuri na sanya su fito da dukkan makamansu da kan sa hatta wanda bai damu da nazari ba, ya gano ‘yan dabdala ne kawai wakilan wadanda ba Musulmi ba kuma ‘yan barandar IPOB. Tsarin mulkin Nijeriya bai hana kowa kafa ƙungiya ko bayyana ra’ayinsa ba amma kar ya zama ƙungiyar ko ra’ayin cin zarafi ne ga wani ɗan aasa mai ‘yanci.
Ina kira ga dukkan al’ummar Arewa mu fito ba fito na fito ba mu wayar da kan juna ta ɓangaren kyakkyawan tarihi da iyayen Lardin su ka gadar kama daga mai girma Firimiya Sir Ahmadu Bello, Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, Chief Sunday Awoniyi, Mr. Micheal Audu Buba, Dokta Ishaya Audu, Malam Aminu Kano, Danmasanin Kano Yusuf Maitama Sule da sauran magabata na kwarai. Haƙiƙa in mu ka kyautata niyya mu ka kuma so juna manyan ƙalubalen da mu ka fuskanta musamman taɓarɓarewar tsaro za su zama sai tashin zance.
