Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Watan Ramadan wata ne mai tsarki da daraja ga al’ummar Musulmi a ko’ina, wanda a cikin sa masu azumi ke shagaltuwa da ayyukan ibada, taimakawa juna, da gujewa faɗa ko tayar da fitina. Sai dai abin takaici da damuwa shi ne a bana al’ummar Musulmi sun gudanar da ibadar azumin Ramadan cikin fargaba da tashin hankali, musamman a Nijeriya da wasu yankunan Gabas ta Tsakiya, inda ake cigaba da luguden wuta tsakanin ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka da kuma Isra’ila.
A Nijeriya, yankin arewacin ƙasar nan na cigaba da shiga tasku daga hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, da kuma a yankin Arewa maso Gabas, inda ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke cigaba da haifar da matsalar rashin tsaro, ba tare da la’akari da halin da ake ciki na ibada da raunin jiki ba. Musulmi a jihohin Adamawa, Borno, Bauchi, Kebbi, Zamfara, Neja, da Kaduna, sun fuskanci hare-hare daga ’yan ta’adda a lokuta daban-daban, musamman a lokutan buɗe-baki da yayin sallar Asham.
Yanzu da aka shiga rukuni na uku na watan Ramadan, lokacin da al’ummar Musulmi ke fita cikin dare domin halartar sallar Tahajjud a masallatai, don neman dacewa da Daren Laylatul ƙadri, inda a cikinsa ake sa rai da Ubangiji yana amsa addu’o’in bayinSa; akwai fargaba sosai kan tsaron masu sallah da yadda za su samu natsuwar yin ibada.
A yayin da nake wannan rubutu, al’ummar musulmi a garin Jiƙamshi dake ƙaramar Hukumar Musawa a Jihar Katsina, suna kulle cikin gidajensu, saboda fargaba da tsoro, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai garin ranar Talata ana dab da fara buɗe-baki, harin da ya haifar da asarar rayuka uku da jikkata wasu da dama.
Idan ba mu manta ba, a ranar farko ta azumin Ramadan a ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi mahara ’yan bindiga sun kashe mutane 34 da jikkata wasu da dama. Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa a ranar 4 ga watan Maris, ma ana tsakiyar shan ruwa ’yan ta’addan Boko Haram suka far wa barikin sojoji dake Gwoza a Jihar Borno, abin da ya haifar da mutuwar wasu manya da ƙananan jami’an soji, sannan aka kama mata da ƙananan, tare da tarwatsa ’yan gudun hijira dake koma gida gidajensu da gwamnati ta gyara musu, domin su koma su cigaba da rayuwa a garuruwansu.
Daga fara azumin Ramadan zuwa yanzu aƙalla an kai manyan hare-hare a jihohi daban-daban na Arewa har sau shida, ciki har da harin da aka kai sansanin sojoji ta Mayanti a Jihar Borno, a ranar 1 ga watan Maris, inda a nan ma aka kashe Kwamandan sojoji da wasu jami’an sa. An kai irin waɗannan hare-hare a sansanonin sojoji daban-daban cikin Jihar Borno, a wurare irin su Konduga, Kukawa, Bama, Damasak, Marte, Dalwa, Mainok, da kuma Jakana, duk cikin ’yan makwanni ƙalilan. Kuma duk suna kai hare-haren ne a lokacin da akasarin sojoji musulmi ko farar hula suka shagala da shan ruwa bayan buɗe-baki, ko kuma yayin da suke cikin ibada, hankulansu sun koma ga Ubangiji Madaukakin Sarki. Lokacin da suke tunanin musulmi ba su da kuzari ko zafin naman mayar da martani ko gujewa don neman mafaka.
ƙaruwar waɗannan hare-hare sun sanya firgici da damuwa a zukatan Musulmi a jihohin Arewa, duk da ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan bakiɗaya. Dawowar zafafan hare-hare kan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba, a lokacin da ake tunanin an ci galaba kan mayaƙan Boko Haram da ISWAP, kuma a cikin wata mai tsarki na Ramadan babban ƙalubale ne ga tsaron Nijeriya da zaman lafiyarta. Duba da yadda har a wasu wuraren ake samun rahotannin ’yan ta’adda sun ƙwace iko a wasu garuruwa, ko sun kori jama’a sun ƙona garin, yayin da a wasu wuraren ’yan ta’adda ne ke kafa dokoki da sanya haraji ga mazauna yankunan, suna karɓe musu kadarori da dukiyoyi.
Ba zan manta da wani mummunan harin ƙunar baƙin wake da Boko Haram ta kai wajen wani Tafsiri a Jos a ranar 15 ga watan Yuni, 2014 wanda ya haifar da asarar rayuka fiye da 60, yayin wasu da dama kuma suka jikkata. Wannan ta’addanci ba yau aka fara shi ba, kodayake ana samun sauƙi ta wani ɓangaren, sakamakon ƙarin ilimi da gogewa daga jami’an tsaron mu, ’yan agajin mu da sauran jama’a dake ba da gudummawa.
Abin takaici ne ƙwarai da gaske, a ce ’yan ta’addan da suke iƙirarin kafa adalci ƙarƙashin tsarin Musulunci, kamar Boko Haram da ISWAP, su ne kuma suke kai hari kan ’yan uwansu a lokacin da suke cikin masallaci suna ibada, ko suna sauke wani rukuni na shika-shikan da suka gina addinin Musulunci bakiɗaya. Kodayake yawancin su suna kallon sauran musulmi a matsayin kafirai ko waɗanda ba Musulmin gaskiya ba, saboda sun saɓa da irin koyarwarsu. Don haka suke kai musu zafafan hare-hare na mugunta a cikin Ramadan, a ganin su suna koyi ne da Sunna, saboda Manzon Allah (SAW) da sahabbansa sun yi yaƙi a cikin watan Ramadan, lokacin Yaƙin Badar da lokacin Fatahu Makka.
Masu tunanin hakan da suke yi daidai ne, suna aiki ne da gurguwar fahimta da son zuciya, domin su cimma burinsu na tozarta Musulmi da addinin Musulunci. Don haka yana da kyau musulmi su haɗa gwiwa da jami’an tsaro, domin tabbatar da ganin an samar da ƙarfaffan tsari da zai dakatar da waɗannan hare-hare a wuraren ibada da cikin yankunan zaman jama’a a lokacin ibadar Tahajjud, da ma bayan Ramadan. Domin waɗannan hare-hare ba a wannan Ramadan ɗin aka fara su ba, kuma ba lallai bayan sallah su tsaya ba. Mu cigaba da aiki tare muna ƙarfafa junanmu da shawarwari, da dabaru, da gudummawa, domin kawo ƙarshen wannan ta’addanci da ke faruwa.
Kuma kada mu manta a yayin da muke ci gaba da addu’o’i cikin wannan wata da bayansa, mu miƙa kukan kukanmu ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya kawo mana ɗauki mu ga ƙarshen wannan ta’addanci, ba a Arewa da Nijeriya kaɗai ba, da ma duniya bakiɗaya.
