
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta tabbatar da tawagar ‘yan wasanta da za su fafata a Manchester City a wasa na biyu na zangon ‘yan 16 a gasar Zakarun Nahiyar Turai, UEFA Champions League.
Za a buga wasan ne a filin wasa na Etihad da ke birnin Manchester a ƙasar Ingila a gobe Laraba.
Babban labari a wasan shi ne zaƙakuran ‘yan Madrid da ba su samun buga wasan farko ba a yanzu sun dawo cikin tawagar, waɗanda suka haɗa da Kylian Mbappe, Jude Bellingham da kuma Alvaro Carreras.
A wasan farko da aka fafata tsakanin ɓangarorin biyu Madrid ta doke City da ci 3 da 0.
Ga jerin ‘yan wasan da Madrid za ta je da su Manchester kamar yadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo:
Masu tsaron gida:Thibaut Courtois, Andriy Lunin, Fran Gonzalez
‘Yan baya: Dani Carvajal, David Alaba, Trent Alexander-Arnold, Fran García, Antonio Rudiger, Dean Huijsen, Alvaro Carreras, Diego Aguado, Mario Rivas
‘Yan tsakiya: Federico Valverde, Aurélien Tchouameni, Arda Güler, Thiago Pitarch, Cestero, Manuel Angel, Palacios, Eduardo Camavinga, Jude Bellingham
‘Yan gaba: Kylian Mbappe, Vinicius Junior, Gonzalo Garcia, Brahim Diaz, Franco Mastantuono.
