
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno, ta tabbatar da cewa mutane 23 sun mutu, yayin da wasu 108 suka jikkata sakamakon wasu fashe-fashe da suka girgiza Maiduguri a yammacin ranar Litinin, abin da hukumomi suka bayyana a matsayin hare-haren ƙunar baƙin-waken da aka tsara a tare.
Al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7:24, inda aka kai hare-haren a wurare masu cinkoson da muhimmanci a cikin birnin, ciki har da Kasuwar Litinin ta Maiduguri, kofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da gadar sama ta Post Office.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar, binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargi da kai hare-haren ‘yan ƙunar baƙin-wake ne da suka yi amfani da na’urorin fashewa na gida (IEDs).
Yanayin yadda aka kai hare-haren lokaci guda a wurare daban-daban ya sake jawo damuwa kan sabbin dabarun kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke kokarin kawo cikas ga kokarin yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Zagazola Makama, wato masanin harkar tsaro, ya ce zaɓin wuraren da aka kai harin musamman kasuwa, kusa da asibiti, da kuma gadar sama mai yawan zirga-zirga, na nuni da an yi hakan ne domin kara yawan wadanda za su mutu ko su jikkata, yada tsoro, da kuma kawo cikas ga harkokin rayuwa da tattalin arziki a babban birnin jihar.
