Shugaban ƙungiyar Izala reshen Katsina ya buƙaci al’umma su tashi tsaye wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Katsina, Sheikh Dr. Yakubu Musa Hassan, ya yi kira ga ɗaukacin al’umma da su haɗa kai wajen yaƙar safarar miyagun ƙwayoyi da sayar da su, yana mai gargadin cewar matsalar na barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma baki ɗaya.

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin rufe Tafsirin Alqur’ani mai girma na watan Ramadan na bana a Masallacin Modibbo (Kandahar) da ke birnin Katsina.

A cewarsa, yawaitar shigo da miyagun ƙwayoyi cikin al’umma da kuma bazuwarsu a tsakanin matasa na barazana ga rayuwarsu, musamman ganin cewa su ne manyan gobe.

Sheikh Yakubu Musa Hassan ya bayyana cewar, matsalar miyagun ƙwayoyi ta zama babbar annoba saboda yadda wasu mutane ke haɗa kai wajen shigo da su, safarar su da kuma sayar da su a cikin al’umma.

Ya ce, “Babbar musiba ce yadda ake shigo da miyagun ƙwayoyi tare da yaɗa su a cikin al’umma. Akwai masu shigo da su, akwai dillalai, akwai kuma waɗanda ke buɗe shaguna ko gidaje suna sayar da su. Waɗannan mutane suna haɗa kai ne wajen lalata rayuwar matasa waɗanda su ne makomar al’umma.” In ji shi.

Malamin ya jaddada cewar yaƙi da wannan matsala ba aikin jami’an tsaro kaɗai ba ne, illa aikin al’umma ne baki ɗaya domin suna da rawar da za su taka.

“Idan ka san inda ake sayar da miyagun kwayoyi ko waɗanda ke safarar su, amma ka yi shiru ba tare da ɗaukar wani mataki ba, to kai ma ka taimaka wajen lalata al’umma,” in ji shi.

Haka kuma, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya yi kira ga jami’an tsaro da aka ɗora wa alhakin daƙile wannan matsala da su ji tsoron Allah, yana mai gargaɗin cewa akwai zargin wasu jami’ai daga cikinsu na karɓar rashawa daga masu harkar miyagun ƙwayoyi. Ya ce, “Jami’an tsaro su ji tsoron Allah. An ba su amanar kare al’umma daga irin waɗannan abubuwa. Duk wanda ke karɓar kudin haram daga masu wannan harka, ya sani cewa wuta yake tara wa kansa.”

By ukarofi