
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sake rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan Jihar Anambara a karo na biyu a hukumance.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima tare da tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, sun isa filin jirgin sama na Chinua Achebe domin halartar bikin rantsar da gwamnan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, manyan baƙin sun sauka lafiya, inda gwamnatin jihar ta shirya tarba ta musamman domin wannan muhimmin biki.
An gudanar da bikin ne a filin Alex Ekwueme Square, wanda aka gyara kwanan nan. Manyan mutane daga sassa daban daban na ƙasar nan sun halarta, ciki har da dattawan ƙasa da sarakunan gargajiya daga al’ummomi 179 na jihar da ma wasu daga sauran jihohi.
Haka kuma, jam’iyyar APC ta tattara magoya bayanta daga dukkan mazaɓu 326 domin shaida wannan gagarumin biki.
A wani ɓangare, an tsaurara matakan tsaro a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin.
Jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda, NSCDC da FRSC sun bazu a wurare masu daban-daban.
Gwamna Soludo da mataimakinsa sun riga sun kammala wa’adinsu na farko, inda wannan na yanzu zai fara aiki daga yanzu har zuwa 2030.
