2027: Hon Alaku ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta faɗaɗa hukuncin cire David Mark zuwa matakin jihohi

Spread the love

Daga JOHN D WADA, a Keffi

A yayin da duka jam’iyyun siyasa daban-daban a ƙasar nan ke cigaba da shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2027 da ke tafe, shugaban babbar jam’iyyar adawar nan da ake kira African Democratic Congress (ADC) a jihar Nasarawa, Hon. Godwin William Alaku ya buƙaci babbar kotun ɗaukaka ƙara ta gaugauta yanke irin hukuncin nan da ta yanke na dakatar da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar na ƙasa wato sanata David Mark akan kujerar sa wajen dakatar da duka ire-iren sa dake jihohin ƙasar nan da ƙananan hukumomi dama yankunan gundumomi.

Hon. Godwin William Alaku yayi kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a garin Sabon-Gida dake jihar Nasarawa jim kaɗan bayan kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke hukuncin dakatar da David Mark din da sauran mukarrabar sa a matakin ƙasa kwanan nan.

Yace tabbas akwai wannan tsari da shugabannin kwamitin jam’iyyar ADC din na riƙon kwarya a matakan jihohi da ƙananan hukumomi da kuma gundumomin jihohin nan da suma yakamata kotun ta dakatar dasu kamar yadda aka yi wa David Mark ɗin don a doka ba a san da su ba kuma tuni wa’adin riƙon ƙwaryar nasu da suke ikirari da shi ya riga ya ƙare.

Ya cigaba da bayyana cewa” Ka ga so nake a madadin dukanmu ainihin shugabannin jam’iyyar mu ta ADC a jihohin ƙasar nan da aka san mu, inaso nai amfani da damar nan don inyi kira na musamman ga kotun ɗaukaka ƙara na tarayya dake Abuja wadda a kwanan nan ta yanke hukuncin dakatar da tsohon shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar mu ta ADC wato shi sanata David Mark cewa akwai ire-iren mutane dake riƙe da wannan irin muƙamin sa a matakin jihohin ƙasar nan da ƙananan hukumomi da kuma gundumomi da suma tunda aka cire na sama suma yakamata hakan ya shafe su.

“Don kaga waɗannan mutane sun zo ne sun same mu a jamiyyar ta ADC wato bayan anyi merja kenan inda maimakon subi tsarin mu na fara yin ragistar zama mambar jam’iyyar a gundumomin su da ƙaramar hukumar su da sauran su amma sai suka ƙi yin haka inda suka naɗa wa kansu waɗannan muƙamai na kwamitin riƙon ƙwarya kamar dai yadda shi David Mark yayi aka dakatar da shi.

“Saboda haka ina kuma kira agaresu ire-iren mutanen musamman a nan jihar Nasarawa da sauran duka jihohin ƙasar nan baki ɗaya cewa babu wanda ke korensu daga jam’iyyar, suna da damar zama mambobin mu bayan sun cika duka sharuɗɗan jam’iyyar ADC din.” Inji shi.

Daga nan sai shugaban jam’iyyar ta ADC a jihar Nasarawa, Hon. Godwin William Alaku ya kuma yi amfani da damar inda ya buƙaci duka mambobin jam’iyyar a jihar da ƙasa baki ɗaya da sauran hukumomi da suka dace su cigaba da yin watsi da waɗannan shugabannin kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar a matakan jihohi da ƙananan hukumomi da kuma gundumomin don a cewarsa a yanzu suna aiki ne a matsayin ‘yan boge don doka bata yarda da su ba kamar dai yadda yake ƙunshe a shari’ar da ta yi sanadin cire David Mark ɗin inda ya nanata cewa akwai sananne da halatattun shugabannin jam’iyyar ADC ɗin a jihar a yanzu da ke ƙarƙashin jagorancin sa kuma haka lamarin yake a sauran jihohin ƙasar nan baki ɗaya.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne babbar kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin tarayya Abuja ta yanke wani hukuncin siyasa da yayi sanadin cire shi tsohon shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na babbar jam’iyyar adawar a matakin ƙasa kwanan nan inda kotun ta bayyana cewa sam David Mark din da muƙarrabar sa din basu cancanta da muƙamin ba kafin a yanzu shi kuma Hon. Godwin William Alaku wato ainiyin shugaban jam’iyyar a jihar Nasarawa da sauran shugabannin a sauran jihohin ke kiran kotun ta faɗaɗa hukuncin zuwa jihohin da ƙananan hukumomi da kuma gundumomi baki ɗaya don tsaftace jam’iyyar.

By ukarofi