Ƙaramar Sallah: Jakadun ƙasashen ƙetare 17 suka halarci bikin hawan sallah a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Jakadun da suka sauka Katsina ƙarƙashin jagorancin jakadar ƙasar Belgium Mr Peter Leenknegi sun sami tarba daga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa da mataimakin sa da sauran manyan jami’an gwamnati.

Gwamnan ya wuce da jakadun zuwa fadan Sarkin Katsina da ke Kofar Soro a Katsina inda a kai bikin hawan Sallah.

Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman da tawagar sa suka fara iso Kofar Soro suna sanye da tufafin gargajiya da yaba jakadun da dubban mutane sha’awa.

Haka kuma manyan hakimai fiye da 50 da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya wanda kowannen su sun ci kwalliya ga kowane tare da makaɗa da masu busa algaita na gaban hakimai akan hanyar su ta kai gaisuwar ban girma ga mai martaba sarkin Katsina.

Bayan kammala bikin hawan Sallar, Gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranci jakadun zuwa fadar Gwamnati jihar,bayan nan gwamnan ya kai jakadun wuraren tarihi a Katsina.

Haka kuma ana sa ran za su kai ziyarar ban girma fadar sarakunan Katsina da Daura kafin su bar Katsina.

Haka kuma ranar hawan bariki ake sa ran Sarkin Katsina zai kai ziyarar Barka da Sallah ga gwamnan jihar Malam Dikko Raɗɗa a inda Sarkin da kuma gwamnan za su gabatar da jawabi.

Jakadun sun haɗa da na ƙasashen Turai da na Nahiyar Asiya da suka halarci hawan Sallar.

By ukarofi