Daga USMAN KAROFI
Hukumar yaki da rashawa da sauran laifukan da suka shafi rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta sanar cewa za ta kawo tsohon Gwamna Nasir El-Rufa’i gaban kotu a ranar Talata mai zuwa a Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai yana tsare tun bayan ya amsa kiran hukumar EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, inda aka yi masa tambayoyi na tsawon awanni 48 kafin ICPC ta ɗauke shi hannunta.
Tsawaita zaman tsarewar El-Rufai ya haifar da cece-kuce, inda ƙungiyoyi da mutane da dama suka buƙaci a gurfanar da shi a gaban kotu ko a sake shi. Kakakin ICPC, John Okor Odey, ya bayyana cewa El-Rufai zai fuskanci shari’a a kotun ƙoli ta tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, ƙarƙashin lambar shari’a FHC/KD/73/2026, wanda ke da tuhuma da suka haɗa da satar dukiyar jama’a da kuma wanke kuɗaɗe.
Haka kuma, wata shari’a daban da aka ɗauki lamba KDH/KAD/ICPC/01/26, wanda ICPC ta shigar a Kotun Ƙoli ta Jihar Kaduna, ya haɗa El-Rufai da Malam Amadu Sule (LEDA), inda ake zarginsu da cin zarafi a ofis, damfara, niyyar yin damfara, da ba da fifiko ba bisa ƙa’ida. ICPC ta shigar da dukkan tuhumar a ranar 18 ga Maris, 2026, yayin da ranar gurfanarwa a kotun jihar za a sanar da ita daga baya.
