An naɗa C.P Aliyu Umar Fage sabon kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sabon kwamishinan, ya karɓi ragamar aiki daga tsohon kwamishinan yan sanda CP Bello Shehu wanda likkafar sa tayi gaba zuwa mataimakin sufeton ‘yan sanda na ƙasa.

Ana sa ran sabon jagoran zai kawo sababbin dabaru da tsare-tsare da za su ƙarfafa yaƙi da aikata laifuka, tare da inganta hulɗa tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Al’ummar jihar na fatan sabon kwamishinan yan sandan zai yi amfani da ƙwarewar sa domin kawo ƙarshen matsaloli rashin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar musamman a birnin Katsina inda wasu gungun matasa da aka fi sani da ƙauraye suka addabi mutane.

Haka matsalar dillancin miyagun ƙwayoyi wanda kusan ya zama ruwan dare a jihar.

Mutanen na nuna ayar tambaya kan yadda dillalan ƙwayoyi da masa taammali da ƙwayar suka ƙaru dukkan kasancewar hedkwatar jami’an hukumar NDLEA a Katsina.

By ukarofi