Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa, Nijeriya tana buƙatar aƙalla Dala biliyan 100 domin magance matsalolin da suka dabaibaye fannin samar da wutar lantarki a ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa wannan adadi mai girma ba zai samu nan take ba, sai dai ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zuba jari masu zaman kansu, a matakai daban-daban.
A cewarsa, ɓangaren samar da wuta kaɗai na buƙatar kusan dala biliyan 30 domin ƙara samar da megawatt 20,000 na lantarki, inda kowace tashar megawatt 1,000 ke cin kusan dala biliyan 1.5.
Ya ƙara da cewa, ɓangaren jigilar wuta kuma na buƙatar kusan dala biliyan 20 domin tabbatar da isar da wutar da aka samar yadda ya kamata.
Haka zalika, ɓangaren rarraba wuta ma na buƙatar irin wannan adadi, yayin da bangaren iskar gas — wanda ke da muhimmanci wajen samar da lantarki — ke buƙatar sama da dala biliyan 22 domin gina bututun gas.
Ministan ya ce, idan aka haɗa dukkan wadannan fannoni — na sama (upstream), na tsakiya (midstream), da na ƙasa (downstream) — jimillar jarin da ake buƙata ya haura dala biliyan 100, abin da ke nuna girman ƙalubalen da ke gaban ƙasar.
Duk da haka, Adelabu ya bai wa ’yan Nijeriya tabbacin cewa za a fara ganin sauyi a harkar wutar lantarki cikin makonni biyu masu zuwa, sakamakon inganta samar da iskar gas.
Ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka haddasa ƙarancin wuta shi ne rashin biyan kuɗaɗen da kamfanonin samar da wuta ke bin masu samar da gas.
Ya ce, “Idan kana samar da kaya amma ba a biyanka ba, kuma ana tilasta maka sayarwa a farashi mai rahusa, to babu yadda za a yi ka ci gaba da samarwa yadda ya kamata.”
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na bin kamfanonin gas bashin tiriliyoyin naira, lamarin da ya sa suke jan ƙafa wajen samar da iskar gas ga tashoshin wutar lantarki.
Dangane da gyaran tsarin farashin wuta, Adelabu ya ce sauye-sauyen da aka fara tun 2023 sun fara haifar da ɗa mai ido, inda aka samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga a fannin duk da matsalolin kayan aiki da ke rage saurin ci gaba.
Ya ƙara da cewa, samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 a rana a Nijeriya abu ne mai yiwuwa, sai dai yana buƙatar lokaci da kuma cikakken tsarin da zai ɗore.
Wannan ne ya sa gwamnati ta ƙaddamar da tsarin farashin wuta da ya dace da kasuwa ga wasu masu amfani da lantarki, kusan kashi 15 cikin 100, inda ake iya samar musu da wuta tsakanin awa 20 zuwa 24 a kullum.
A ƙarshe, ministan ya jaddada cewa warware matsalolin wutar lantarki a Nijeriya na buƙatar haɗin kai, tsare-tsare masu inganci, da kuma juriya wajen aiwatar da gyare-gyare masu ɗorewa.
