Tarayyar Turai ta fitar da tallafin Yuro miliyan 288 domin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tawagar Tarayyar Turai (EU) a Nijeriya da ECOWAS ta sanar da fara aiwatar da wani babban shirin tallafi na Yuro miliyan 288 domin ƙarfafa muhimman sassa na tattalin arzikin ƙasar, ciki har da lafiya, noma, kuɗaɗe, ƙaura, sauyin yanayi da kuma gina kayayyakin more rayuwa na fasahar zamani.

An bayyana wannan shiri ne a yayin taron ministoci na EU da Nijeriya da aka gudanar a Abuja, inda aka yi bayani kan yadda za a rarraba tallafin a matsayin gudunmawa da kuma tallafin bunƙasa tattalin arziki.

Babban Darakta na Hulɗa da ƙasashen Duniya na Hukumar Tarayyar Turai, Stefano Signore, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin EU na haɓaka zuba jari ƙarƙashin tsarin Global Gateway, wanda ke da nufin bunƙasa tattalin arziki da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya bayyana cewa, duk da irin nasarorin da aka samu, har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙoƙari musamman a fannoni kamar lafiya da noma, domin inganta ƙa’idoji, kayayyakin more rayuwa da kuma samar da masana’antu na cikin gida.

Haka kuma, ya jaddada cewa EU za ta ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tafiyar da batun ƙaura ta hanya mai ɗorewa, tare da samar da damar rayuwa mai kyau ga waɗanda suka dawo ƙasarsu.

A nasa jawabin, Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya ce wannan haɗin gwiwa ya samo asali ne daga tattaunawar dabarun EU da Nijeriya ta 2023, wadda ta zama wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.

Ya ƙara da cewa, wannan haɗin gwiwa na nuna zurfafa alaƙa da jajircewar ɓangarorin biyu wajen gina kyakkyawar hulɗa mai ɗorewa, wadda ta dogara da mutunta juna, ci gaba tare da zuba jari mai amfani.

Bagudu, wanda Doris Anite-Uzoka ta wakilta, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki masu zurfi domin daidaita tattalin arziki, ƙarfafa tsarin kuɗi da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari.

A nasa ɓangaren, Manajan Darakta kuma Shugaban Bankin Masana’antu, Olasupo Olusi, ya ce wannan haɗin gwiwa na nuna yadda dabarun haɗin gwiwa za su iya jawo dogon zuba jari a muhimman sassa na ƙasa, musamman lafiya da noma.

Shi ma Daraktan ƙasa na Gidauniyar Gates a Nijeriya, Uche Amaonwu, ya jaddada muhimmancin tallafa wa masana’antar kiwon lafiya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen cimma manufofin haɗin gwiwa na ci gaba.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin Yuro miliyan 288 da aka ware, akwai rabon da ya haɗa da Yuro miliyan 23 don tallafin kayayyakin dijital na gwamnati, da Yuro miliyan 108 da suka haɗa da tallafi da rance ga gwamnatin Nijeriya. Haka kuma, Yuro miliyan 50 an ware su domin tallafa wa masana’antar kiwon lafiya ta hanyar Bankin Masana’antu, yayin da Yuro miliyan 85 za su tallafa wa harkokin noma, musamman a sassan kiwo da coco.

Bugu da ƙari, akwai Yuro miliyan 16 da za a kashe wajen ƙarfafa tsarin kula da harkokin ƙaura, tare da mayar da ‘yan ƙaura gida da kuma yaƙi da safarar mutane da fasa-ƙwauri.

Wannan shiri na EU ana sa ran zai taimaka wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi, mai jure ƙalubale, tare da samar da dama ga al’umma a fannoni daban-daban na rayuwa a Nijeriya.

By ukarofi