Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi a ƙarshen cinikayyar ranar 20 ga Maris, 2026, inda farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 8.22 cikin ɗari zuwa Dala 112 a kowacce ganga a duniya. Wannan lamari ya ƙara tsananta matsin lamba a kasuwar makamashi tare da jefa damuwa kan makomar tattalin arzikin Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan tashin farashi ya kai sama da kashi 53 cikin ɗari cikin watan Maris kaɗai, sannan ya haura kashi 83 cikin ɗari tun farkon shekarar nan. Babban abin da ya haifar da wannan hauhawar shi ne rikicin da ke ci gaba tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran, wanda ya haddasa tangarɗa a samar da mai a duniya.
Bayanai daga shafin petroleumprice.ng sun nuna cewa matatar mai ta Dangote ta sauya farashin man fetur har sau biyar cikin watan Maris sakamakon sauye-sauyen kasuwar duniya. A farkon watan, farashin ya tashi daga naira 774 zuwa naira 874 a kowace lita, sannan ya ci gaba da ƙaruwa zuwa naira 1,050, daga nan zuwa naira 1,175, sai naira 1,245, kuma daga bisani ya kai naira 1,275.
Haka kuma, farashin jigilar mai a yankunan bakin teku ya tashi daga naira miliyan 1.512 zuwa sama da naira miliyan 1.646 a kowace metric ton, lamarin da ke nuna yadda kasuwar ke fuskantar matsin lamba mai tsanani.
A birnin Legas, gidajen mai na kamfanin MRS sun ƙara farashin lita da naira 100 zuwa naira 1,367, yayin da a Abuja kamfanonin Ranoil, Empire Energy da AA Rano suka daidaita nasu farashin zuwa naira 1,440, naira 1,430 da kuma naira 1,370 bi da bi.
Babban Daraktan kamfanin Financial Derivatives Company, Bismarck Rewane, ya bayyana a taron tattalin arziki na shekarar 2026 da aka gudanar a Legas cewa tashin farashin man fetur na riga ya fara tasiri kai tsaye ga kuɗin sufuri da kuma farashin kayayyaki.
Ya ce, “Kowane ƙarin kashi ɗaya cikin ɗari na farashin mai na jawo karin kashi 0.079 cikin ɗari a kuɗin sufuri da hauhawar farashi. Idan aka yi la’akari da yadda farashin mai ya ƙaru da kusan kashi 42 cikin ɗari a wannan wata, akwai yiwuwar ƙarin hauhawar farashi da zai kai tsakanin kashi uku zuwa huɗu cikin ɗari nan da watanni biyu zuwa uku masu zuwa.”
Ya kuma yi gargaɗin cewa wannan matsin lamba na iya sa Babban Bankin Najeriya ya ɗauki matakin taka-tsantsan wajen tsara manufofin kuɗi, maimakon rage ribar ruwa, har sai an samu daidaito a kasuwa.
Rahotanni sun nuna cewa kuɗin sufuri da jigilar kaya sun ƙaru da kusan kashi 20 cikin ɗari, abin da ke ƙara wa ’yan kasuwa nauyi a daidai lokacin da suke fama da tsadar gudanar da kasuwanci, ƙarancin buƙata da kuma sauyin darajar kuɗi.
Haka kuma, hauhawar farashin abinci ta haura kashi 12 cikin ɗari a duk shekara, kamar yadda Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta bayyana, lamarin da ke ƙara matsa wa al’umma wajen tafiyar da rayuwa.
Masana sun yi nuni da cewa wucewar farashin Brent sama da dala 93 a farkon watan ya nuna cewa ana fuskantar matsalar samar da mai, kuma wannan sabon tashin farashi na iya ƙara dagula hauhawar farashi a ƙasashe irin su Nijeriya da ke dogaro da shigo da man da aka tace daga waje.
