Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihar Legas ta yi fintinkau, inda ta zama a kan gaba cikin jerin jihohin da suka fi karɓar kaso mai tsoka na kuɗaɗen shiga na tarayya da aka raba a watan Janairu 2026, bisa kuɗaɗen da aka tara a watan Disambar 2025.
Rahoton da aka fitar ya nuna cewa Legas ta samu jimillar Naira biliyan 55.83, wanda ya kai kashi 7.9 cikin zari na Naira biliyan 706.47 da Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya raba wa jihohi 36 na ƙasar.
Babban abin da ya ƙara wa Legas wannan kaso shi ne yawan kuɗaɗen harajin ƙarin darajar kayayyaki (VAT) da ta samu, wanda ya kai Naira biliyan 50.12. Wannan ya nuna ƙaruwa mai yawa idan aka kwatanta da Naira biliyan 25.21 da ta samu a watan Disamba, da kuma Naira biliyan 40.07 na watan Nuwamba.
A matsayi na biyu, Jihar Delta ta karɓi Naira biliyan 47.15, ciki har da Naira biliyan 11.43 na VAT. Ita kuwa Jihar Akwa Ibom ta zo ta uku da Naira biliyan 35.89, inda rabon VAT ya kai Naira biliyan 10.82.
Sai dai wasu jihohi sun kasance a ƙasan jadawalin rabon kuɗaɗen. Jihar Ogun ta samu Naira biliyan 12.78 (ciki har da Naira biliyan 10.01 na VAT), Kuros Riba ta karɓi Naira biliyan 12.64 (VAT Naira biliyan 8.72), yayin da Jihar Ekiti ta fuskanci abin mamaki inda aka nuna cewa rabonta ya zama na ragi, wato Naira biliyan -6.69, duk da cewa ta samu Naira biliyan 8.96 na VAT.
Binciken da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa gaba ɗaya an raba Naira tiriliyan 2.59 ga matakai uku na gwamnati daga kuɗaɗen shiga na watan Disamba 2025.
Daga cikin wannan adadi, Naira tiriliyan 1.63 sun fito ne daga asusun doka, Naira biliyan 39.91 daga harajin canja kuɗi ta lantarki (EMTL), yayin da Naira biliyan 913.96 suka fito daga VAT.
Dangane da rabon, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 653.50, jihohi 36 sun karɓi Naira biliyan 706.47, yayin da kananan hukumomi 774 suka samu Naira biliyan 513.27.
Haka kuma, an ware Naira biliyan 96.08 ga jihohin da ke samar da man fetur daga asusun kashi 13 na hakar albarkatun ƙasa.
Rahoton ya ƙara da cewa hukumomin tattara kuɗaɗen shiga sun samu kuɗaɗen gudanar da aiki, inda Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta samu Naira biliyan 27.85, Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS/NRS) ta karɓi Naira biliyan 53.12, yayin da Hukumar Kula da Haƙar Man Fetur (NUPRC) ta samu Naira biliyan 23.72.
Wannan rabon kuɗaɗe na FAAC na ci gaba da nuna yadda tattalin arzikin ƙasa ke tafiya, tare da bayyana rawar da haraji, musamman VAT, ke takawa wajen ƙarfafa kuɗaɗen shiga na jihohi.
