Jami’ar Dan Fodiyo za ta karɓi baƙuncin taron Tarihi da Waƙoƙin Muhammadu Bawa Dan’anace

Spread the love

Daga MUHAMMAD HABIB ALHASSAN

Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sokoto ta yi shirin gagarumin taron ƙasa kan tarihi da waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa, a Waiwayen Shekaru Arba’in masu Tarin Abubuwan Tunawa a Kansu. 

Yanzu haka waɗari ke gudana babu kama hannun yaro a shirye-shiryen amsa kiran Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sokoto zuwa wajen gagarumin taron ƙasa a kan Tarihi da Waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa a Waiwayen Shekaru Arba’in Masu Tarin Abubuwan Tunawa a Kansu. 

Wata sanarwa daga Malam Adamu Yunusa Ibrahim, Sakataren kwamitin Shirya taron ta nuna cewa ana kuwa tsinkayar biyan kuɗin sabulun kwalliyar taron bisa hasashe ya yi tagomashi da armashin samu halartar manyan malamai, masana da ma’abota shauƙin cigaban harshen Hausa da adabi da al’ada. Ya ƙara da cewa sune masu bayyanawa da sharhantawa da jinjina kan wannan taliki da ya tsayu a matsayin wani gunkin waƙar Hausa, haziƙin mawaƙin da baitocinsa ke ci gaba da zaburar da jaruntaka da ƙarfin hali a zukatan mayaƙa da masu sha’awar gadon adabin Hausa. 

Malam Adamu Yunusa Ibrahim ya ce a Babban Zauren Taro na Mazaunin Dindindin na Jami’ar, a tsawon kwanaki uku, kowace rana daga ƙarfe tara na safe, daga ranar Jumu’a 3 zuwa Litinin 6 ga watan Afrilun shekarar nan miladiyya ta 2026 taron zai gudana, in-sha-Allah, a Shugabancin Maigirma Katukan Yauri Alhaji Abubakar Sadiƙ Yalwa, Manajan Daraktan Hukumar Raya Yankunan Samar da Wutar Lantarki ta Ruwa ta ƙasa (N-HYPPADEC), a kulawar Babban Mai Masaukin Baƙi, Farfesa Bashiru Garba MFR, Shugaban Jami’ar Usmau ɗan Fodiyo ta Sokoto, da taimakawar Farfesa Salisu Ahmed Yakasai, Daraktan Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami’ar.

Haka kuma, kamar yadda takardar gayyata ta nuna, Maigirma ɗanmadamin Birnin Magaji Alh Ibrahim Muhamad Birnin Magaji (mai kirari ‘Gani Nan Bari Nan, Arzikin Alawa Masu ƙwarjinin Baibayar Allah’) shine Babban Mai Gabatar da Jawabin Buɗe Taron mai take Dambe Wasan Maza, Kowa YaYi Hankali Ya Barka: Tarihin Rayuwa da Gudummawar Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa Ga Harshen Hausa da Adabi da Al’adun Hausawa. 

Inji Sakataren Kwamitin Shirya Taron, masu gabatar da Jagaban Maƙalu kuwa sune Talban Bunun Kano Farfesa Ibrahim Garba Satatima daga Sashen Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero ta Kano, da Farfesa Bashir Aliyu Sallau Sarkin Askar Yariman Katsina/ Hakimin Safana daga Sashen Harsunan Najeriya na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, da Farfesa Sulaiman Adamu Sarbi daga Sashen Harsuna da Al’adun Nahiyar Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria.

Babban Baƙo na Musamman shine Mai Girma Gwamnan Sokoto Alhaji Ahmad Aliyu, Phd, tare da Babba Baƙo Mai Girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sokoto). Haka kuma, wani abin ƙari armashin taron shine karimcin halartar Mai Alfarma Sarki Musulmi Alhaji Muhammadu a matsayin Babban Uban Taro, a yayin da zai samu rufa bayan Uwayen Taro da suka haɗa da Mai Martaba Sarkin ɓurmin Bakura Injiniya Bello Muhammad Sai da Sarkin Mafara Alhaji (Dr) Bello Muhammadu Barmo, da Masu Girma Uwayen ƙasar ’Yarkofoji da Gandi da ‘Yartsakkuwa da Raɓah da Wurno da kuma Achida.

By ukarofi