Algaita Tv ta kalli halin da Kannywood ke ciki ne ta taimake ta – Darakta Mu’azzam Yari 

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A daidai lokacin da aka samu sauyin shugabanci a tashar talabijin ta ALGAITA TV wadda take haska finafinan Hausa na masana’antar Kannywood bayan saukar shugaban ta na farko Umar Sani Kofar Mazugal inda aka maye gurbin sa da sabon shugaba Mu’azzam Idi Yari. A yanzu haka an samu wasu canje-canje da kuma ci gaban tashar domin tafiyar da ita daidai da bukatar al’umma. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da sabon shugaban Mu’azzam Idi Yari domin bayyanawa masu karatu inda alkiblar ALGAITA TV ta sa a gaba, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Mu’azzam Idi Yari kai ne sabon shugaban tashar talabijin ta ALGAITA TV a yanzu, don haka za mu so ka yi wa masu karatu bayani a game da ita tashar talabijin ta ALGAITA TV tun farkon samuwar ta da kuma halin da take ciki a yanzu.

MU’AZZAM: To Alhamdulillah a yanzu da nake a matsayin Manaja a wannan tashar talabijin ta ALGAITA TV zan iya cewa ina da masaniya a kan asalin ta da kuma samuwar ta, don haka ita ALGAITA TV an kafa ta ne a shekarar 2024 kunsa ƙarshen shekarar wadda a yanzu ta kusa shekara biyu kenan. Kuma daman ita wannan tashar ta ‘yan Kannywood ce da wasu masu kishin masana’antar suka samar da ita, kuma daman tun a baya sun daɗe suna bayar da gudunmawa a cikin masana’antar don haka sun ga abubuwan da ita masana’antar take buƙata musamman lokacin da aka fara shirya finafinai masu dogon zango, don haka ya kamata a ce masana’antar tana da gidan talabijin da zai zama madubin al’umma wajen fitar da finafinan da suke yi domin a ga ci gaban su. 

Wannan ya sa suka yi ƙoƙarin da kuɗinsu suka samar don su taimaka wa masana’antar.

A yanzu da yake an shafe sama da shekara guda tashar tana gudanar da aikin ta. Ko wanne irin canji ta samar?

To daman kamar yadda na faɗa ita ALGAITA TV ta kalli masana’antar ne da kuma halin da take ciki don haka suka zuba kuɗinsu domin su taimaki masana’antar. Domin akwai wasu abubuwa da suka faru a baya tun bayan mutuwar kasuwancin CD sai abin ya koma kame-kame wasu su yi fim su saka a YouTube wasu kuma saboda kowa ya gani su kan nemi wani gidan talabijin din a saka musu wanda kuma biya ake yi kuɗaɗe masu yawa don haka sai ka biya kuɗin za a haska maka.

Hakan sai ya zama furodusa yana shan wahala wajen ya nemo kuɗi ya yi furodusin sanan ya nemo kudin da za a haska masa. To hakan sai ya zama an samu wani ƙalubale ta yadda idan ka yi fim ɗin sai ka nemo tallan da za a saka wanda idan ka yi haka kuɗin da kai aikin fim din da kuɗin da za ka biya a saka maka a talabijin ɗin to shi kansa tallan da ka nemo ka saka ba zai fitar da kai ba. Don haka sai ya zama ana shan wahala. Masu ƙoƙarin ne za su haye da kyar. To sai wasu masu kishin masana’antar suka ga cewar mai zai hana a samar da gidan talabijin namu na Kannywood a tallata shi ta yadda duk wani furodusa da ya je ya samo kuɗin sa ya zuba harkar fim ya je ya samo tallan da zai saka to ga gidan talabijin ya samu da zai saka masa wanda kuma ba kuɗi zai karɓa ba za a yi ne a kan wani tsarin da za a taimaki juna.

Wannan ya sa daga buɗe tashar talabijin ɗin sai manyan furodusa na Kannywood suka zo suka karɓi tafiyar, don haka ake ganin tashar talabijin ta ALGAITA TV ta zo da farin jini. Shi ya sa ake ganin kowa so yake a haska fim ɗin sa a tashar talabijin ta ALGAITA TV duk ‘yan Kannywood sai suka ɗauka tashar tasu ce. Saboda da haka wannan nasara ce babba, kuma masana’antar Kannywood ta ɗauki alƙibla duk da a baya akwai waɗanda suka yi yunkurin samar da haka, amma sai suka kasa. To yanzu bisa gaskiya an samu haɗin kai mai kyau tsakanin furodusa da su waɗannan masu gidan talabijin ɗin saboda yadda suka nuna talabijin din na ‘yan Kannywood ne, don haka mu ma sai muka tsaya domin mu taya su samar da ci gaba da kuma bunƙasa masana’antar.

Za mu ci gaba a makon gobe insha Allah.

By ukarofi