Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar kula da tsaro da harkokin sufuri ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta fara daukar tsauraran matakai kan mutanen da ke zubar da yashi, ƙasa, tsakuwa, kayan gini ko wasu kayayyaki a kan hanyoyi a faɗin Jihar Katsina.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri, ya fitar a madadin babban shugaban hukumar, Manjo Garba Yahaya Rimi mai ritaya.
Sanarwar ta bayyana cewa, yadda ake zubar da irin waɗannan kayayyaki ba tare da tsari ba a kan hanyoyin jama’a, ya zama ɗaya daga cikin manyan dalilan haddasa haɗurra, barazana ga lafiyar al’umma, da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.
Hukumar KASSAROTA ta kuma gargadi jama’a da su daina wannan ɗabi’a wadda ta saɓa wa doka, tare da jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci daidai da tanadin doka.
Hukumar ta kuma buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ke toshe hanya ta hanyar layin domin daukar mataki tare da tabbatar da tsaro duk masu amfani da hanyoyi.
Hukumar KASSAROTA ta na nan tsaye da ƙafafunta wajen kare rayuka da kuma tabbatar da ingantacciyar lafiyayyar zirga-zirga a fadin Jihar Katsina
