
Ƙungiyar ISWAP ta tabbatar da mutuwar wani babban mambanta na Majalisar Shawara (Shura Council), mai suna Abu Yahya Al-Muhajir, inda ta bayyana hakan a matsayin bbabban ashi ga ƙungiyar.
An bayyana hakan ne a cikin wata takardar yaɗa farfaganda da ƙungiyar ta fitar, inda ta yi alhinin rasuwar sa tare da kiran mutuwar tasa a matsayin “mafi girman rashi a kwanakin
A kwanan nan ne a yankin Malam Fatori majiyoyin tsaro sun ce ana danganta Al-Muhajir da hare-haren da aka kai a yankin Tafkin Chadi (Lake Chad Basin),
Saidai har yanzu ba a tabbatar ko an kashe shi ne yayin wani hari da ya gaza a Malam Fatori ba ko kuma sakamakon harin sama da aka kai a yankin ba.
Majiyoyin sun ƙara da cewa, sojoji sun dakile harin da ISWAP ta kai a Malam Fatori, inda aka kashe kimanin mayaƙa 80 na ƙungiyar yayin fafatawar da kuma hare-haren biyo baya.
Sun kuma bayyana cewa, bayanan cikin gida na ƙungiyar sun nuna cewa Al-Muhajir ko dai ya samu raunuka masu tsanani yayin harin da bai yi nasara ba, ko kuma ya mutu ne daga baya sakamakon raunukan da ya samu bayan hare-haren soji.
Rahotanni daga Nigerian Armed Forces & Military News sun nuna cewa harin da ya gaza na ranar 18 ga Maris, 2026 ya yi sanadin mutuwar kusan mayaƙa 84 na ISWAP, yayin da wasu da dama suka jikkata.
