Tinubu ya sadaukar da baki ɗaya albashinsa ga sojoji tun bayan zama shugaban ƙasa

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa sojojin Nijeriya musamman waɗanda suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan waɗanda da suka rasa rayukansu bai wa ƙasa kariya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin bikin cikar sa shekaru 74 da haihuwa, inda ya ce wannan mataki wata hanya ce ta girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar da sojoji ke yi wa kasa.

A cewar sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya umarci Akanta-Janar na Tarayya da ya bude wani asusu na musamman domin wannan shiri. Asusun zai rika bayar da tallafi ga sojojin da suka jikkata, da kuma zawarawa, mazajen da matansu suka rasu, da ‘ya’yan wadanda suka mutu a bakin aiki.

A wani ɓangare na nuna kudurinsa, shugaban ya yi alkawarin bayar da dukkan albashinsa tun daga lokacin da ya hau mulki a matsayin gudunmawar farko ga asusun, domin tabbatar da cewa ba a manta da wadanda suka sadaukar da rayuwarsu ba wajen samar da zaman lafiya da tsaro.

Tinubu ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, kamfanoni masu zaman kansu, abokansa da sauran masu fatan alheri da su mara wa wannan shiri baya. Ya ce za a bayyana cikakken bayani kan yadda asusun zai gudana nan gaba kadan.

By Babaji