Uba Sani, Pantami, Ɗangote, Atiku da wasu sun halarci jana’izar mahaifiyar El-Rufa’i a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Birnin Tarayya Abuja ta cika da sanannun ‘yan siyasa a jiya Lahadi yayin da aka yi jana’izar Hajiya Umma, mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

An sallace ta ne a babban masallacin Juma’a na ƙasa dake Abuja, inda aka haɗu wajen yi mata addu’o’in fatan samun rahamar Allah.

Cikin waɗanda suka halarci sallar akwai Alhaji Aliko Ɗangote, Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, NSA Nuhu Ribadu, Atiku Abubakar, Gwamna Senator Uba Sani , Gwamna Zulum, Bago, Abdulazeez Yari da sauran tsofaffi da shuwagabanni, Gwamnoni, Sanatoci, Sarakuna, Yan kasuwa da sauran su.

Da fari Shugaba Bola Tinubu, Nuhu Ribaɗu da Shugaban jam’iyyar, Farfesa Nentawe Yilwatda sun miƙa gaisuwar ta’aziyyarsu bisa babban rashin ga tsohon ministan birnin tarayyar.

By Babaji