Kotu ta ayyana 14 ga Afrilu a matsayin ranar hukunci akan buƙatar belin El-Rufa’i

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu, 2026 domin yanke hukunci akan buƙatar beli da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar.

A yau Laraba ne lauyoyin El-Rufa’i da masu gabatar da ƙara wato hukumar ICPC suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotun da ke Kaduna domin duba batun bukatar ba da tsohon gwamnan na jihar Kaduna beli.

Babban lauyan masu kare El-Rufai, Adewole Iyamu, ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar samun sakamako mai kyau, yana mai cewa sun gabatar da dukkan hujjojinsu yadda ya kamata a gaban kotu.

Ya tabbatar da cewa an gabatar da buƙatar belin a hukumance, kuma bangaren masu kara sun mayar da martani akan bukatar.

Haka kuma, ya ce ana sa ran El-Rufai zai gurfana a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 10 ga watan Afrilu kan wata kara daban da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta shigar.

A cewarsa, ɓangaren wanda ake kara sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sauraron ƙarar ranar 10 ga Afrilu, inda ya ce sun riga sun shigar da dukkan takardun da ake buƙata akan al’amarin.

By Babaji