Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya amince da naɗin sabbin hakimai uku a masarautar.
Waɗannan mutane uku duk ‘ya’yan asalin zuriyar Sarki Muhammadu Dikko ne, iyali da suka shahara da kyakkyawar al’ada ta nagarta, hidima da jagoranci a Katsina da ma Nijeriya baki ɗaya.
A wata takardar buƙatar haka daga Majalisar Masarautar Katsina wacce Alhaji Isah Ali Kankia, Sakataren Majalisar Masarautar ya sanya wa hannu, an aikawa mai bai wa gwamna shawara kan harkokin masarautu.
Hakimai uku da za a naɗa sun haɗa da Alhaji Ahmad Abdulmumini Kabir Usman – Hakimin Dankama (Ɗan-Majen Katsina) – Ɗan Mai Martaba Sarkin Katsina, sai Alhaji Muhammad Dikko Umar – Hakimin Raɗɗa (Gwagwaren Katsina) – Ɗan Malam Dikko Umaru Raɗɗa, Gwamnan Jihar Katsina da Alhaji Abubakar Dardisu, FCNA, mni – Hakimin Muduru (Sarkin Mudurun Katsina).
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na shirya bikin, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan amincewa.
Ya kuma jaddada cewa kwamitin zai tabbatar da cewa bikin ya kasance mai cike da daraja, al’ada da muhimmancin al’adu irin na wannan lokaci.
A farkon makon gobe za ayi bikin naɗin sarautar a fadar Sarkin Katsina.
