ADC tsagin David Mark ta caccaki INEC kan matsayarta ga hukuncin kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, ta caccaki matsayar Hukumar Zaɓe (INEC) dangane da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara akan rikicin shugabancin jam’iyyar.

A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar a jiya Laraba, ya zargi hukumar zaɓen da miƙa wuya ga matsin siyasa.

Ya kuma yi zargin cewa matsayar INEC ɗin ta yiwu ne saboda rashin jituwa da ke tsakanin gwamnati da ADC, yana mai cewa hakan wani yunƙuri ne na daƙile tasirin ‘yan adawa da samar da tsarin jam’iyya ɗaya a Nijeriya.

Bolaji Abdullahi ya, bayyana kalaman INEC a matsayin abin da ba a gina ba akan tsari, yana mai cewa hakan ya ci karo da haƙiƙanin al’amari da kuma salon gudanar da aiki a tsarin da dokar ƙasa ta gindaya.

Kakakin ADCn ya ƙara da cewa, a yanzu jam’iyyar tana nazari akan zaɓin da take da su kuma nan ba da jimawa ba za ta bayyana matakinta na gaba yadda ya dace da tsarin doka.

Kazalika, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da magoya baya da su cigaba da kwantar da hankula yayin da ake ƙoƙarin warware matsalolin shari’ar shugabancin a hukumance.

A ranar Laraba INEC ta ce, daga yanzu ba za ta sake sauraron tsagin David Mark ko Nafiu Bala ba akan lamuran jagorancin ADC, bisa la’akari da nazari da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 12 ga watan Maris.

By Babaji