
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suak yi yunƙurin kai wa a yankin Hyeipang da ke Jos a Jihar Filato, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar daƙile harin da kuma cafke mutum ɗaya da ake zargi da hannu aciki.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a daren Lahadi a ƙauyen Pwomol da ke gundumar Heipang, inda aka kai farmaki kan matasa yan sa-kai da ke tsaron al’umma. Wani mutum ɗaya ya jikkata kuma yana karɓar magani a asibiti.
Haka kuma, a safiyar Litinin, an kashe wani makiyayi a ƙauyen Jol da ke ƙaramar hukumar Riyom, yayin da aka ce an yi masa kwanton ɓauna tare da ɗan uwansa, wanda ya samu tserewa.
Kungiyoyin ƙabilun yankin sun zargi juna da hannu a hare-haren, sai dai kowanne ɓangare ya musanta zargin da ake masa.
Da yake magana a madadin al’ummar yankin, wani jagora mai suna Suraj Tijjani ya ce mazauna sun kimtsa cikin hanzari a yayin da suka samu bayanin sirri akan wasu miyagu na shirin kai musu farmaki.
