
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro da aiki a ƙarƙashin rundunar atisayen HADIN KAI sun yi nasarar kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya yi ajalin wata budurwa a yankin Ngomari da ke Jihar Barno a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, lokacin da wasu jami’an tsaro na sa-kai, waɗanda ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma, su ka yi harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’Adua.
Rahotanni sun bayyana cewa harbin ya yi sanadin suɓutar hannu, inda wani harasashi ya kauce ya bugi budurwar, kuma ta mutu nan take.
A wata sanarwa da Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa cikin gaggawa dakarun Operation HADIN KAI, tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force, sun bi sawun waɗanda ake zargi har suka kama su.
Ya ƙara da cewa, a halin yanzu waɗannan mutane suna tsare a hannun sojoji, kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace don cigaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu bisa tanadin doka don tabbatar da adalci akan lamarin.
