
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane biyu ne suka rasu yayin da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa bom akan hanyar Lumma-Babanna da ke Ƙaramar Hukumar Borgun Jihar Neja.
Al’amarin ya faru ne da misleading ƙarfe 2 na rana a ranar Lahadi, wanda ya yi ajalin wani direba da wani matuƙin babur da ya rasu bayan fashewar bom ɗin.
A cewar hukumomi, direban yana ƙoƙarin neman wata hanya ce domin ficewa daga yankin a lokacin da al’amarin ya faru sakamakon hawa kan abin fashewar da motarsa ta yi, wanda ya haddasa mummunan iftila’i.
An gano cewa, ta hanyar ake bi sakamakon lalacewa da gadar da ta haɗa Lumma-Babanna da Jamhuriyar Benin ta yi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasu Abiodun ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya baya ga dasa bom da maharan suka yi, sun kuma ta yin harbe-harbe a yankin.
