
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Bankin Nijeriya CBN, ya yi watsi da rahoton ƙarya da ke iƙirarin gabatar da sabuwar tsabar kuɗi ta Naira 5,000.
Manhaja ta ruwaito cewa, an nuna takardar tsabar, wadda ta karaɗe shafukan sada zumunta ɗauke da hoton Shugaba Bola Tinubu.
Wannan iƙirarin ya haddasa cece-kuce acikin masu amfani da kafafen musamman wajen tafka muhawara game da sahihancinta.
Saidai, babban bankin ta kafar X, ya ƙaryata rahoton, inda ya ce na bogi don haka al’umma su faɗaka.
A shekarar 2025 ne CBN ya ƙaryata cewa ya samar da tsabar Naira 5,000 da 10,000 don sauƙaƙa hada-hadar kuɗaɗe, yana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya.
