Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Katsina ta kammala shirye-shiryen gudanar da auren gata na farko ga amare da angwaye 2,000 da aka zaƙulo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta ce idan komai ya tafi daidai, za a gudanar da auren gatan na farko a Jihar Katsina a ranar 25 ga Afrilu, 2026.
A yayin wani taron horaswa kan rayuwa da kuma shawarwari da aka shirya wa masu cin gajiyar shirin, shugabar gidauniyar tallafin aure ta al’usra, Malama Murja Ibrahim Duwan, ta bayyana cewa horon na nufin bai wa sabbin ma’auratan da aka tantance ilimi da ƙwarewa da kuma muhimman dabaru da za su taimaka wajen samun nasarar rayuwar aure.
Ta ƙara da cewa za a ba su takardun shaidar kammala samun horo a matsayin sharaɗin shiga auren gatan.
Shi ma darakta-janar na hukumar hisbah ta Katsina, Dakta Aminu Usman Abu-Ammar, ya ce shirin auren gatan na daga cikin matakan gwamnati na rage yawaitar munanan ɗabi’u a cikin al’umma.
Ya bayyana cewa akwai mata zawarawa, marayu da kuma masu rauni da ke son yin aure amma rashin ƙarfin tattalin arziki ya hana su. Ya ce shirin zai bai wa amaren tallafi, haka kuma an tanadi kayan tallafi ga kowane ango domin sauƙaƙa rayuwarsu.
A nata jawabin, kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana cewa dukkan sabbin ma’auratan su 2,000 sun riga sun yi gwaje-gwajen lafiya da tantancewar kafin aure.
