Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Matar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta raba kayan abinci ga mutane musamman mata su 600 masu rauni a ƙarƙashin shirin sabunta fata wato Renewed Hope Initiatiɓe.
Da take jawabi a taron da aka gudanar a cibiyar bajekolin kasuwanci ta jihar Zamfara dake a Gusau jiya Alhamis, uwargidan shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta ce, an samar da tallafin ne don taimaka wa marasa galihu a faɗin ƙasar.
A cewarta, shirin wani ɓangare ne na bunƙasa zamantakewa ta hanyar shirin wayar da kan jama’a a ƙarƙashin shirin sabunta fata na gwamnatin tarayya.
Uwargidan shugaban ƙasar wadda matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima ta wakilta ta ce, shirin zai ci gaba a faɗin jihohi 36 na ƙasar nan.
Da take jawabi a wurin taron, matar gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta sake jaddada ƙudurin gwamnatin mijinta wajen inganta rayuwar mutane masu rauni musamman mata da yara ƙanana a jihar.
Ta yaba wa Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu bisa goyon bayan da take bai wa mata da yara a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiatiɓe a jihar.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa matan gwamnoni sama da goma sha huɗu suka halarci ƙaddamar da shirin.
