Dimukraɗiyyar Nijeriya tangal-tangal take yi?

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA

A cikin tsarin mulkin dimukraɗiyya, ana ɗaukar adalci, bin doka da kuma bai wa kowane ɗan ƙasa damar bayyana ra’ayinsa a matsayin ginshiƙai na ci gaba da zaman lafiya. Dimukraɗiyya ba wai kawai tsarin zaɓe ba ne bisa doron siyasa, a’a, illa wata hanya ce ta tabbatar da cewa ikon mulki yana hannun jama’a, tare da damar sauya shugabanni cikin lumana da gaskiya.

Sai dai a ’yan shekarun da suka yi ƙasa da uku, ana ci gaba da tayar da ƙura game da yadda wasu ke ganin gwamnatin jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki ke ƙoƙarin karkatar da tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Wannan zargi ya ta’allaƙa ne kan yadda ake kallon cewa ana amfani da wasu hukumomin gwamnati da suka kamata su kasance masu zaman kansu wajen murƙushe ‘yan adawa da rage tasirinsu a siyasa.

Dimokuraɗiyya tana buƙatar cikakken ‘yanci ga ‘yan siyasa da al’umma domin su yi muhawara, su yi takara, su kuma bayyana ra’ayoyinsu ba tare da tsoro ba. Haka kuma, tana buƙatar hukumomi masu zaman kansu waɗanda za su yi aiki bisa gaskiya da adalci, ba tare da son zuciya ko tasirin siyasa ba.

Idan waɗannan abubuwa suka lalace, tsarin dimokuraɗiyya zai fara samun rauni. Wannan ne ya sa masana siyasa da masu sharhi ke nuna damuwa kan abin da suke gani a matsayin alamu na koma-baya a wannan fanni.

ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen da ake yi shi ne amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kamar EFCC da ICPC wajen bibiyar ‘yan adawa, yayin da ake zargin wasu masu alaƙa da gwamnati ba sa fuskantar irin wannan matsin lamba.

Da yawa suna bayyana ra’ayin cewa: An fi mai da hankali kan binciken ‘yan adawa, wajen kamawa da gurfanarwa a kotu a matsayin makamin siyasa. Yayin da ake zargin jinkirta ko watsi da wasu shari’o’i idan sun shafi ‘yan jam’iyya mai mulki.

Wannan lamari, idan har yana faruwa, yana iya haifar da rashin amincewa da hukumomin gwamnati, tare da raunana tsarin adalci.

Kotuna su ne ginshiƙin tabbatar da doka a kowace ƙasa. Amma idan aka fara zargin cewa ana amfani da su wajen cimma burin siyasa, hakan na iya haifar da babbar matsala.

A wasu lokuta, an ga yadda rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun adawa ke ƙarewa a kotu, inda ake zargin cewa wasu hukunce-hukuncen suna amfani da ɓangaren da ke da kusanci da gwamnati.

Masu sukar wannan hali na cewa: Ana amfani da kotuna wajen sauya shugabancin jam’iyyu, kuma ana tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun adawa. Idan kotu ta rasa cikakken ‘yancinta, to dimokuraɗiyya na fuskantar babbar barazana.

Wani zargi kuma shi ne cewa ana ƙoƙarin haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa domin rage ƙarfinsu. Wannan na iya faruwa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da: Tallafa wa wasu ɓangarori a cikin jam’iyya domin su yi rikici da kuma yin amfani da matsin lamba na shari’a ko tattalin arziki wajen raunana shugabanni.

Wannan yanayi yana sa jam’iyyun adawa su kasa tsayawa da ƙafafunsu, wanda hakan ke rage ingancin dimokuraɗiyya.

Idan aka bar irin wannan zargi ya ci gaba, zai iya haifar da matsaloli masu yawa, ciki har da: Rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe da haddasa ƙaruwar rashin zaman lafiya da kuma rage sha’awar shigar matasa cikin harkokin siyasa.

Sauran matsalolin da abin zai iya haifarwa akwai koma-baya a ci gaban dimokuraɗiyya, sannan ƙasa ba za ta iya samun ci gaba ba idan babu adalci da gaskiya a harkokin siyasa.

Ko da wane ɓangare mutum yake, abu mafi muhimmanci shi ne kiyaye tsarin dimokuraɗiyya. Don haka, akwai buƙatar: Tabbatar da cikakken ‘yancin hukumomin gwamnati da guje wa amfani da ƙarfi wajen murƙushe ‘yan adawa. ƙarfafa dokoki da za su kare ‘yancin jam’iyyu. Da ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin dimokuraɗiyya.

Haka kuma, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula suna da rawar takawa wajen fallasa da kuma kare gaskiya.

Dimokuraɗiyya ba ta ginuwa a rana ɗaya, haka kuma ba ta rushewa a rana ɗaya. Amma tana buƙatar kulawa, gaskiya, da adalci domin ta ɗore.

Zarge-zargen da ake yi game da tsangwamar ‘yan adawa da amfani da hukumomi wajen murƙushe su, ko da kuwa gaskiya ne ko a’a, suna nuna cewa akwai buƙatar a ƙara ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

A ƙarshe, makomar ƙasa tana hannun shugabanni da al’umma baki ɗaya. Idan aka rungumi gaskiya, adalci, da bin doka, to Nijeriya za ta iya zama abin koyi a Afirka. Amma idan aka bari siyasa ta rinjayi doka, to hakan na iya jefa ƙasa cikin mawuyacin hali.

Dimokuraɗiyya tana buƙatar kowa ya taka rawarsa, gwamnati, ‘yan adawa, kotuna, da kuma talakawa, domin tabbatar da cewa ƙasa ta ci gaba cikin lumana da ci gaba mai ɗorewa.

Amma a irin wannan yanayi da ake ciki, sai nake ganin dimokuraɗiyyar tana tangal-tangal, har ina tunanin anya dumokuraɗiyya za ta ɗore a Nijeriya?

By ukarofi