Karfafa gwiwar matasa kan ci gaban fasahar zamani 

Spread the love

Masana ɗabi’ar ɗan adam sun bambanta tsakanin mai canjin tunani da wanda tunaninsa ba ya sauyawa. Duk wanda tunaninsa ba ya sauyawa shi ne mai dogara akan wani, domin samun tallafin gudanar rayuwa. Ko kuma wani abin tinƙaho da kowacce dama da yake da ita. Wannan halin ya ƙara tsawaita ne a shekarun da ake fama da lalacewar harkokin siyasa, da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da kuma gurɓacewar ɗabi’u da al’adu.

Cigaba a canjin tunani na nufin burin mutum ya canza daga yanayin da yake ciki ko kuma ya bunƙasa yanayin aikinsa daga natsuwa zuwa ga wani sabon yanayin da mutum zai wahala, kafin samun nasara. A dalilin haka sai ƙara samun ilimi da dabara akan aikin da yake ciki. Cigaba ba ya zuwa cikin sauƙi, dole sai mutum ya wahala kuma ya sha suka daga wajen jama’a. Cigaba na gaske na buƙatar ƙarfin hali, ba ragwanci da tsoro ba. In mutum yana so ya samu ƙwarewa a aiki ko kuma wata fasaha ta musamman, kamar yadda a wannan zamani aka samu ci gaban fasahar sadarwa ta zamani, wacce ta zama tamkar walkiya mai haskaka ko ina, dole sai ya yi haƙuri da duk wata jarabawa da zai fuskanta, a rayuwarsa.

Irin wannan tunani na cigaba shi ke sa mutum ya koyi abubuwa da dama, ko kuwa neman ilimi, ko ƙarin haske ko da kuwa a wajen waɗanda ka taɓa koyar da su ne a baya, ko waɗanda ka girme su. Ci gaban tunani shi ke sa mutum ya yaɗa abin da ba shi da cikakken sani akai, musamman a inda ƙwararru suke, domin ya koyi abin da bai sani ba. Wani lokacin mai ilimi kan fasahar zamani na iya maka isgilanci a kan rashin ganewarka da wuri. Wani sa’in fasahar zamani na iya tozarta rashin wayewar ka. Idan har ka iya jurewa waɗannan matsaloli za ka samu nasara da ci gaba a harkokin rayuwa.

Ba da, jimawa ba, tashar BBC Hausa ta wallafa wani faifan bidiyo na wani almajiri mai suna Rabi’u Halliru wanda mutane suka san shi da Likitan Farce. Wannan almajiri ya kasance yana da ci gaba a canjin tunani. Bai dankwafar da kansa a irin mawuyacin yanayi na ƙasƙanci da wulaƙanci da almajirai ke samun kansu a ciki ba. Almajirai na fuskantar ƙalubale da yawa, wani lokacin ma suna fuskantar barazanar fyaɗe, wasu kuma na zama makami da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen kai hare-haren da ta’addanci akan mutane.

Duk da yanayin da Rabi’u ya samu kansa, amma ya gina wa kansa rayuwa bisa ga tafarki mai kyau. Dan kuɗaɗen da ya samu a wajen yankan ƙumba ya inganta sana’arsa ta hanya tsaftace sana’arsa ta hanyar samar da akwatin da yake adana kanyan aikinsa, har da rigar aikinsa da yake sakawa kamar irin ta likitoci. Rabi’u ya gama sakandire kuma burinsa shi ne wata rana ya zama likita na gaske. Da fatan za a samu masu tausayi da halin da za su taimaka masa, domin cika masa burinsa.

Abin lura a nan shi ne, ire-iren su Rabiu masu ci gaba a canjin tunani suna da yawa a ƙasar nan, amma babban abin da ya fi ci masu tuwo a ƙwarya shi ne basu da waɗanda za su ƙarfafa musu gwiwa ko kuwa basu agajin da ya dace domin cimma burinsu. Wannan na cikin manyan dalilan da suka sa wani lokaci ’yan uwan mu na kudancin Nijeriya suke mana kallon cewa yankin Arewa ba shi da wani abin ci gaba in banda tashe-tashen hankula da kashe-kashen mutane.

A wannan zamani na ci gaban fasahar zamani da muke ciki, akwai nau’ikan fasaha iri-iri wanda matasan Arewa suka koya, waɗanda kuma za su iya bunƙasa rayuwar su, kuma su samar wa kansu cigaba. Zaman kashe wando da ƙwacen wayoyi da sauran harkokin ta’addanci za su ragu. Daga cikin abubuwan da matasan mu za su amfana da su a harkokin fasahar zamani akwai; ilimin zane-zanen na’ura mai ƙwaƙwalwa (Graphic design), ilimin tace hotunan bidiyo (Video Editing), tallace-tallacen zamani a shafukan sada zumunta (Digital marketing), ilimin amfani da shafukan sada zumunta domin inganta kowanne irin aiki ko kasuwanci (Social media management) da sauran su. Bugu da ƙari, yankin kudancin Nijeriya matasan su sun tsunduma wajen koyar waɗannan fasahohin zamani fiye da yankin mu na Arewa. Hakan ya samu ne domin masu magabatan su ba gwamnati da masu zaman kansu suna ƙarfafa musu gwiwa, samar musu da jari da ɗaukar nauyin ba su horo, don samar musu da sana’o’in dogaro da kai.

Haka zalika, yana da muhimmanci ga matasan Arewa su kasance masu canjin tunani. A kullum mutum ya kasance yana tunanin yaya zai inganta kasuwancin sa ko sana’arsa ko kuwa amfani da ilimin sa ta hanyar da fasaha zamani za ta inganta masa harkokin rayuwarsa. Harwayau, masu ruwa da tsaki a Arewa suna da nasu kaso wajen ƙarfafa wa matasan Arewa ta fasahar zamani domin ciyar da yankin gaba. ƙarfafawa ya ƙunshi sama wa matasa hanya ko kuwa tallafa musu da kuɗaɗe ko wata hanya da za ta karfafa musu gwiwa wajen samar wa yanki Arewa ci gaba mai ɗorewa. 

Sannan a ƙarshe, gwamnati ta samar da ma’aikatu na horar da matasa akan sana’o’i da fasahar zamani ko ta zuba jari ta hanyar tallafa wa kowanne matashi da ke da hazaƙa da kuma ci gaba a tunani domin kawo wa yankin Arewa da kuma Nijeriya ci gaba mai ɗorewa. 

Hassan Imran ya aiko da wannan wasiƙa ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected].

By ukarofi