Mai ƙabilanci zai riga rana faɗuwa

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Masu iya magana na cewa gaskiya ba ta neman ado kuma duk daren daɗewa ko an kaucewa gaskiya sai an dawo kanta. Kazalika ita kuma ƙarya fure ta ke yi ba ta ’ya’ya. Wani salon, wai saƙo na isa inda a ke buƙata, a a waye waye sai ya mulki kansa ko za a kori wasu mutane daga ƙasar su koma inda su ka fito, duk na fitowa ne daga ‘yan bazata maƙiya Hausawa, Musulunci da Arewa. Na sha haska mu ku mutanen nan kuma akasarinsu ma ba su taba taka jihohin da a ke samun ƙalubalen tsaro ba. Hasalima dai miyagun mutanen nan, na zaune ne a garuruwan da a kan tare hanya a yanka Hausawa da sauran Musulmi matafiya. Na kawo dalilan da ke nuni da Bazatawa na nuna su na da mabiya addinin Musulunci, kirista da ma gargajiya, amma sam ba haka lamarin ya ke ba, don kacokan ajanda ce ta waɗanda ba musulmi ba kuma burinsu kawai yaki da Musulunci ne ta hanyar zagin duk shugabannin musulmi da kau da kai daga duk wuce gona da iri na waɗanda ba Musulmi ba.

Musayar baƙaƙen maganganu da zunduma ashar a yanar gizo na zolayar Bazatawa da tunanin ko ma duk sun gama da Arewa saura kwasar ganima. Duk wannan farafaganda a shafukan yanar gizo ne don kuwa ‘yan ƙalilan kashi 1% da ke rajin wannan tafiya, na shiga taitayinsu a duk lokacin da kafafen labaru na gaskiya ke zantawa da su. Maimakon zagi da kunna wuta kamar za a kife duniya, sai ka ga su na kaucewa amsa tambaya da yin kame-kame har ma murmushin makirci su ke yi. Ko a mafarki ba wanda ya isa ya shiga kowane gidan rediyo ko talabijin a jihohin arewacin Arewa ya zagi Shehu Mujaddadi, Sir Ahmadu Bello ko wani babban malamin addini. Idan kuma sun yi mu su, su gwada.

Har yau sai dai a wajen ‘yan bazata na ke ganin su na tallata wasu ‘yan takara da sunan shirin zaben 2027 a doron ƙabilanci. Manyan ‘yan takarar da na ga hotunansu dama sun sha lashe zaɓe kuma su na kan kujera a yanzu haka, amma ba su taba fitowa sun yi kamfen ta hanyar kabilanci ba. Su kan nemi ƙuri’un talakawa ne karankataf ba kamar yadda Bazatawa ke neman bata mu su suna ba. Duk wanda ya ke son ya riga rana faɗuwa zaɓe, ya gwada biyewa ƙaryar ‘yan bazata. Holoko hadarin kaka kenan. Mu je zuwa mahaukaci ya hau kura.

Shawarata mu guji biyewa kwangilar maƙiya Arewa don ba mu san inda toka ke tsada ba, balle mu yi garajen ƙona rumbunmu. Ba za mu zuba ido ‘yan rajin Biyafara da maciya amanar addinin Kirista su fake da batun tsaro, su na ɗinka rigar Hausawa ta bogi don murƙushe yankin da Shehu ya feshe da addu’ar arziki da ‘yan uwantaka ba.

A iya sani na kuma tabbas ina cikin waɗanda za su iya magana kan ɗan majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa tsawon shekaru da mu ke tare kasancewar ba ya gudun zantawa da manema labaru; bai taɓa ayyana kansa da hulda da ‘yan iƙirarin Hausa zalla ko wata ƙungiya da ke farfaganda a madadinsu ba. Jama’a mun san akasarin karnukan farautar mutanen nan na amfani ne da sunayen ƙarya kamar Bahaushe waye waye Al waye waye amma dai su na fitowa kullum su na yayata wannan farafaganda da cin zrafin jama’a, murɗe wuyan tarihi da kanbama rashin tsaron Arewa ta hanyar kirkirar hotuna na manhajar AI don fito da hoton yankin tamkar kaburbura ne kawai su ka saura ba wani abun alheri da a ke yi. Ga su nan rike da wayoyi a hannunsu, su na shagali a birane da kauyukansu na banza 7 ɗin zamanin yau amma sai ka ga wani dan sullutu ya yi wuf ya rubuta “…yanzu haka za mu zauna sai sun karar da mu…” Wani ma matashin sai ya sha lemon kwalba ya yi gyatsa sannan sai ya fara rubuta karya. Irin wannan kan iya yaɗuwa don yadda dandalin yanar gizo ya ke ba da dama ga waɗanda ba su da kan gado su rubuta duk abun da su ka ga dama su sake ba tunanin wani zai cutu ko za a iya samun matsala daga labari marar tushe. Haƙiƙa wannan na da bambanci da kafafen labaru na keke da keke da ke da jami’in tacewa da rairaye bayanai don fidda labaru masu sahihanci.

A cikin duk waɗanda su ka kwan biyu a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa na daga wadanda kan kawo min ziyara har ofis mu zanta ko ma mu fita don duba wasu lamura na labaru. Na rubuta wannan sako a fili ne don iya gaskiyar kenan. A yadda na san halinsa indai ya na tare da masu ruruta fitinar ƙabilanci a Arewa zai fito ya bayyanawa duniya. Haƙiƙa waɗannan mutanen masu tunanin akwai Bahaushe daban da sauran jama’ar Arewa na kawo hoto da sunan dan majalisar a shafukansu don haka ina kira a gare shi ya taka mu su birki don ba su da manufa mai kyau fiye da shuka ƙiyayyar da za ta iya haddasa fitinar da ba wanda zai tsara a Arewa. 

Tabbas Yariman Burumburum na girmama sarakunan Arewa, na daukar Sir Ahmadu Bello Sardauna a matsayin jigon Arewa. In mun duba Shehu Usmanu da kullum su ke aibatawa da murde wuyan tarihinsa, haƙiƙa Ado Doguwa na ɗaukarsa babban jagora na addini. Mai alfarma sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar uba ne gare shi kamar sauran ‘yan siyasarmu na Arewa. Dabi’un ‘yan zalla sun yi hannun riga kakaf da yadda Alhassan Ado ke rayuwa. Wallahi a ido na na ga yadda ya ke girmama wani mai sarauta kuma cikin wadanda ‘yan zalla ke zagi. Na zo wucewa a Transcorp Hilton, haka Ado ya ja hannuna irin “Nasiru ina ka shiga ne..” ya ja hannuna ya kai ni wajen basaraken ya gabatar da ni mu ka gaisa. Mai irin wannan halin ne zai zama wakilin ‘yan wargaza Arewa? ƙarya su ke yi ta hanyar shigar burtu.

Ko a bara lokacin da a ka yi taron majalisar shari’a ƙarƙashin Dokta Bashir Aliyu, ai Ado Doguwa ne ya wakilici kakakin majalisa Tajuddeen Abbas kuma ya yi bayanai masu gamsarwa da mara baya 100% ga manufofin shahararrun malaman na Islama har ma da alwashin kai bayanan majalisa don sanya hakan a doka. Ciki har da hana labarun karya ko yin ɓatanci haka kurum ga masu mutunci. Na kawo labarin a shafin nan. A lokacin ba irin cin mutunci da alkaba’i da ‘yan zalla ba su yi wa manyan malamai da su ka halarci taron ba. Kun ga duk masu cin zarafin malamai a doron ƙabilanci akwai babbar ayar tambaya kan addinin da su ke bi.

Haka ma don rashin sanin bambancin majalisar shari’a SCSN, majalisar ƙoli ta Musulunci NSCIA da JNI, sun dauka Sultan ne ya jagoranci taron, alhali gayyatarsa a ka yi kuma bai samu halartar taron ba mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Bamalli ne ya wakilce shi. Duk da haka sai da su ka ƙirƙiro hotonsa daga wani taro su ka yi ta aibata shi. Sultan dattijo ne bai ce uffan ba don ina ganin ya dauka wasu matasa ne ‘yan Arewa ke neman fandarewa da za a iya shawo kan lamarin ta wa’azi. Ai wadannan ba ruwansu da malaman nan don addininsu ma ba daya ba ne.

‘Yan iƙirarin nan sun so su ja sunan Garkuwan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa cikin farafagandarsu. Wallahi ba ruwansa da su. Shin a shafin nan sau nawa na kawo zantawar bidiyo da Garkuwa kan lamuran raya Arewa. A lokacin da a ka fara samun rashin jituwa a masarautar Kano, Garkuwa ne mutum na farko a manyan Arewa da ya yi magana ta lallai a warware rashin jituwar don duk abun da ya taɓa masarautar Kano ya shafi Arewa kakaf. Ko ‘yan watannin baya ya jagoranci kafa wata kungiyar hada kan Arewa a Kaduna kuma na saka faifan a shafin nan. Tun wajajen 2003, Garkuwa ya gabatar da wani jawabi a taron gwamnonin Arewa kan lamuran tsaro inda ya ba da shawari kan yadda za a iya magance matsalar kafin ta kai yadda ta ke. An maida jawabin ya zama littafi kuma ina da littafin.

KAMMALAWA

Gaskiyar magana babu ɗaya daga mutanen nan biyu da zai jingine Arewa a gefe ya biyewa wasu masu ajandar wargaza yankin da fakewa da batun tsaro don haddasa yaƙin ƙabilanci da shaidanci. In Allah ya yarda duk zan kawo mu ku faifan bidiyo ba ma sauti ba, na nesanta bayin Allah daga makircin ‘yan zalla. Shin Bahaushe Musulmi, kai mu je ma ko Kiristan kirki zai zama sana’arsa kunna wutar ƙabilanci da sunan tsangwamar Bahaushe a ka yi ya dau matakin? Wallahi Bahaushe ke mulkin kansa ba ma a Arewa ba, a duk inda ya ke a duniya. Duk wanda ya ke kururuwar Bahaushe ya mulki kansa to tabbas ba Bahaushe ba ne dan shigar burtu ne mai buya a wayar salula don cimmawa maƙiya Arewa muradunsu na wargaza ƙarfin yankin a siyasa, addini da tattalin arziki.

By ukarofi