Yadda ya kamata ƙungoyin addini su tallafawa mabiyansu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na karanta wani nazari da wani ya yi game sa ƙoƙarin da wata ƙungiyar Kirista take yi don inganta rayuwar mabiyanta da bunƙasa samar da hanyoyin shigar kuɗaɗenta. Wannan tsari nasu ya ja hankalina matuƙa, kuma na ga dacewar in kawo batun nan, domin ni da ku mu yi nazarinsa. Mu kuma duba yiwuwar kawo wani sauyi makamancinsa a cikin ƙungiyoyin mu na addini da cibiyoyin ilimi da nazari, ta yadda za mu samu hanyoyin inganta rayuwarmu.

Al’ummar mu ta Arewa na cikin wani mawuyacin hali na talauci, jahilci da rashin tsaro, musamman a tsakanin musulmi. Lallai babu shakka muna buƙatar gudunmawar masana da manazartan mu, har ma da attajiranmu kan yadda za mu samar wa kanmu mafita. Mu fita daga ƙangin da muke ciki.

Bayanin da zan kawo a nan ƙasa na rairayo shi ne daga wani rubutu, kamar yadda na faɗa a baya, wanda wani Kirista, Chukwudi Iwuchuku, mabiyin majami’ar Christ Embassy ya fitar, inda ya yi sharhi kan nasarori da tsare-tsaren da majami’ar ta samar, waɗanda suka cimma tsawon shekaru, sakamakon amfani da dabaru da arziƙin ƙwararru da suke da su a cikin mabiyansu.

A nazarin da ya yi ya gano, majami’ar na da wani ɓangare na musamman mai suna, Sashin Kasuwanci (Department of Commerce), wanda ke lura da harkokin kasuwanci na majami’ar. A ƙarƙashin wannan sashi an samar da wani banki mai suna Paralleɗ Bank, wanda ke da lasisi daga CBN, yana kuma da rassa a garuruwa da dama a ƙasar nan. An gano cewa kafin CBN ta ba da lasisin samun damar buɗe banki sai an ajiye biliyoyin nairori da yawansu ya kai kusan Naira Biliyan 200! Yayin da a dukkan rassan majami’ar aka wajabta wa mambobinsu na Nijeriya su buɗe asusu da wannan bankin.

Sannan suna da wani ɓangaren dake kula da kiwon lafiya (Healthcare Management), wanda har ta kai sai da suka mallaki Babban Asibiti mai suna Loɓe World Medical Center, inda duk wata matsala ta rashin lafiya da ta shafi wani mambansu can ake kula da shi. Bayan wannan kuma suna da manhajar da suke musanyar bayanai da sada zumunci ta soshiyal midiya wacce suke kira da KingsChat. Ga kuma manhajar aikawa da kuɗi, ajiya ko rance ta wallet, wanda duk a ƙarƙashin sashin kasuwanci aka samar da ita, wato Kingspay, wacce aka samar ƙarƙashin fasahar Fintech. Mambobin majami’ar suna amfani da ita kamar yadda jama’a ke amfani da Opay da sauran manhajoji makamantansu, inda mutum zai ajiye kuɗi, ya tura kuɗi, ya sayi katin waya da wutar lantarki da sauransu, duka a onlayin.

Waɗannan harkoki na kasuwanci da neman kuɗi, a zahiri ga wanda bai sani ba zai ga ba su da alaƙa da cocinsu, suna gefe suna neman kuɗi, wanda har Musulmi na iya tsintar kansa a cikin harkokinsu. Amma a gefe ɗaya kuma suna gudanar da harkokin addininsu, ba tare da wata matsala ba. Ba sa jira sai lokacin buƙata ya yi a kafa asusun neman taimako ko gidauniya. 

Ban da Christ Embassy, akwai wasu majami’u da suke da wasu tsare-tsare irin waɗannan, irin su ECWA, waɗanda su ma za ka ga suna da asibitoci, makarantu, gonaki, cibiyoyin koyar da sana’o’i, gidajen saukar baƙi, da bankunan taimakon mambobinsu da bashin kuɗaɗe. Kuma suna da rassa a ƙauyuka da birane, inda ɗimbin jama’a ke amfana da su. Kai, har gidan rediyo da talabijin suna da shi, kuma suna nan suna aiki ana amfana da su.

Abin da ya sa na kawo waɗannan bayanai shi ne domin in ƙalubalance mu, musamman mu Musulmi ’yan Arewa, kan samar da irin waɗannan tsare-tsare na yadda al’umma za ta amfana, a inganta iliminsu, lafiyarsu, da kasuwancinsu. Addinin musulunci ba aƙida da tauhidi kawai yake koyarwa ba, addini ne na rayuwa bakiɗaya. Ba zai yiwu a cigaba a yadda ake ba, a duk lokacin da muke da wata matsala ta kuɗi ko wata hidima, sai an yi ta shela ana neman taimakon kuɗi daga hannun mutane, ko kai ko wakilinka. Alhali muna da yawan da za mu iya kafa abubuwan cigaba da za su kawo mana kuɗaɗen da muke buƙata. Muna da ’yan boko da ƙwararrun da za su tsara mana yadda za mu yi, kuma akwai waɗanda suka ƙware wajen gudanarwa, zuba jari, da kasuwanci. Ba sai mun je nema a wani waje ba!

Na san wani zai iya cewa, ai mu ma muna da ƙungiyoyin da suka samar da wasu abubuwa irin wannan kamar su ƙungiyar FOMWAN da Ahmadiyya, da suka samar da asibitoci da makarantu, a garuruwa daban-daban. Akwai kuma ƙungiyar Izala ta ɓangaren Kaduna da na Jos, su ma suna da asibitoci da makarantu, da gidajen saukar baƙi. Amma abin tambaya a nan shi ne a wanne halin yanzu waɗannan wurare ke ciki? Akasarin su, sun durƙushe saboda rashin kyakkyawar kulawa da rashin jagoranci nagari. Asibitoci babu magunguna ba ƙwararrun ma’aikata, makarantun da ake da su babu isassun malamai, kuma yawanci guduwa suke yi saboda babu albashi mai kyau, ko ma dai ba a biya a kan kari. Idan malami ya yi magana sai a ce masa ai aikin Allah ne! Ko kuma idan batun gudanarwa ne sai ka ga an sa waɗanda ba su cancanta ba, saboda kusancinsu da Malam, ko sun daɗe suna yi wa ƙungiya hidima da sauran su. Ba a duba ƙwarewa, da cancanta, don haka ko an samar da abubuwan suke rushewa bayan wasu shekaru.

Akwai ƙungiyoyin Musulunci da suka samar da tashoshin rediyo da talabijin, musamman a matakin satilayit, domin yaɗa koyarwar addini, irin su Sunnah Tɓ, Manara, Wisal, Irshad da sauransu. Amma ba duka ne suke cigaba da watsa shirye-shirye ba, saboda mutanen mu ba kasafai suke iya jure wa irin wannan kasuwancin ba. Ko mun fara rashin gogewa yana sa su gaza. 

Ba zai yiwu mu tafiyar da irin waɗannan muhimman ayyuka kamar yadda muke tafiyar da gidajen mu ko makaratun mu na Islamiyya ba. Dole kowanne fanni a nemi masanansa, kuma a yi aiki da shawarwarinsu. Domin wani lokaci ko da an nemo kwararrun sun ba da shawara, sai daga baya a jingine su a yi yadda aka ga dama.

Ina mai ba da shawara, mu tashi tsaye mu ga cewa, ƙungiyoyin mu na addini, cibiyoyin ilimi da masallatanmu sun zama cibiyoyin gina al’umma, bunƙasa cigaban rayuwa, da inganta tattalin arziki. Mu yi koyi da wasu ƙasashen Musulmi da suka daɗe suna tafiyar da irin waɗannan tsare-tsare, don mu kawo wa al’ummar mu su ma su samu canji a rayuwar su.

Ya kamata a ce, muna tunanin yadda za mu ɗora daga abin da aka fara samarwa, idan makaranta ce daga matakin rainon yara har zuwa jami’a. Idan asibiti ne, a tabbatar an samar daga ɗakin shan magani zuwa asibitin koyarwa. Idan kasuwanci ne, a samar da bankin haɗin gwiwa da taimakon juna, har zuwa cikakken banki na musamman da jama’a da dama za su yi hulɗa da su. 

A nemi ƙwararru da za su ba da shawarwari kan hanyoyin halal na zuba jari, kasuwancin zamani, amfani da fasahar sadarwa, samar da ayyukan yi, da cibiyoyin samar da ilimi da horarwa, don gina al’umma. Ba laifi ba ne gina masallatai da ƙawata su, amma lokaci ya yi da za mu mayar da wasu masallatan zuwa cibiyoyin bincike da nazari. Zan iya tunawa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya sha kira irin wannan, domin ganin cewa a ƙarƙashin tsari na addini mun samar wa al’ummarmu mafita.

By ukarofi