Gaskiyar lamarin harin Jilli – Ministan Tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya fito ya kare harin sama da sojoji suka kai a yankin Jilli da ke Jihar Borno, yana mai jaddada cewa waɗanda aka kashe ba fararen hula ba ne, illa mutanen da ke taimaka wa ’yan ta’adda da kayayyaki da tallafi.

Ministan tsaron bya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a tashar Arise, bayan wani babban taron tsaro da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.

Ya ce, harin ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri, inda aka kai farmaki kan wani wuri da aka sani da cibiyar samar wa ’yan ta’adda kayayyaki.

“Babu wani mara laifi a wurin. Duk wanda yake a can ya san abin da yake yi, kuma yana hulɗa da ’yan ta’adda,” inji shi.

Harin dai ya jawo ce-ce-ku-ce bayan rahotannin da ke cewa an samu asarar rayukan fararen hula, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan dabarun yaƙi da ta’addanci da kuma yadda za a kiyaye rayukan jama’a.

Sai dai Ministan ya ƙaryata zargin kuskure ko gazawar bayanan sirri, yana mai cewa an gudanar da aikin ne cikin tsari da kuma sanin abin da ake yi.

Ya ƙara da cewa, yankin Jilli tuni aka sanya shi a matsayin wuri mai haɗari, inda ’yan ta’adda da masu ba su goyon baya ke haɗuwa domin kasuwanci da musayar kayayyaki kamar abinci, mai da sauran kayan aiki.

“A wannan wuri ba kasuwa ce ta jama’a ba. Wuri ne da ake hada-hadar taimaka wa ’yan ta’adda,” inji Musa.

Ministan ya bayyana cewa wasu na shiga irin waɗannan mu’amaloli ne saboda ribar da ake samu, inda ya ce ana iya sayar da buhun shinkafa har N150,000 a irin waɗannan yankuna, abin da ke jan hankalin masu sana’a duk da haɗarin da ke tattare da hakan.

Ya kuma jaddada cewa duk wanda ya sani kuma ya ba ’yan ta’adda tallafi, ko ta hanyar kuɗi ko kayayyaki, ba za a ɗauke shi a matsayin mara laifi ba a dokokin yaƙi.

“Duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda, to yana cikin su ne. Ayyukansa na ba su damar rayuwa da ci gaba da kai hare-hare,” inji shi.

Sai dai ya bambanta tsakanin waɗanda ake tilasta musu yin aiki da ’yan ta’adda da kuma waɗanda suke aikata hakan da son rai domin riba, yana mai cewa na farko su ne waɗanda ake iya ɗauka a matsayin waɗanda aka cutar.

Game da rahotannin yawan mutanen da suka mutu, Ministan ya nuna shakku kan sahihancinsu, yana tambayar ko akwai hujjoji ko hotuna da ke tabbatar da adadin da ake yaɗawa.

Ya kuma ce shugabannin yankin sun tabbatar da cewa wurin ba matsuguni ba ne na fararen hula, yana mai tambaya: “Idan an kwashe mutane daga wurin, me ya kai wasu can?”

A ƙarshe, Ministan ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin wasu fararen hula da ’yan ta’adda na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke tsawaita rikicin Arewa maso Gabas, yana mai cewa idan aka katse wannan hanyar tallafi, za a samu sauƙin kawo ƙarshen yaƙin.

“Idan mutane suka daina ba su goyon baya, za a kawo ƙarshen wannan rikici cikin sauri,” inji shi.

By ukarofi