Ruwa shi ne ginshiƙin rayuwa — Dan Makwayon Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An bayyana ruwa a matsayin ginshiƙin rayuwa da kuma jigon tafiyar da al’umma, inda aka jaddada cewa har ibada ba ta yiwuwa yadda ya kamata sai da ruwa.

Hakimin Dawakin Kudu, ɗan Makwayon Kano kuma Sakatare na Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakuncin shugabannin kungiyoyin AWASHO da NEWSAN a fadarsa cikin makon da ya gabata.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar Awareness on Water Sanitation and Hygiene Organisation (AWASHO), Kwamarad Yahaya Abdulaziz, ya ce sun ziyarci fadar ne domin sanar da hakimin ayyukan da kungiyoyin ke yi tun daga kafuwarsu.

Ya ce ƙungiyoyin na kokarin wayar da kan al’umma kan muhimmancin shan ruwa mai tsafta, dakile yin bayan gida a fili, da kuma illolin amfani da ruwa marar tsafta.

A cewarsa, an kafa ƙungiyar ne a shekarar 2009, kuma tun daga wannan lokaci ta gudanar da ayyuka da dama tare da hadin gwiwar kungiyoyin kasa da kasa kamar PID, USAID, WISE da UNICEF a kananan hukumomin Dawakin Kudu, Kura, Rogo da Tudun Wada.

Ya ƙara da cewa sun samu nasarori, ciki har da rage matsalar yin bayan gida a fili a kauyuka 20 na karamar hukumar Gezawa, tare da horas da al’umma kan tsaftar ruwa da muhalli.

Sai dai ya bayyana wasu kalubale da suke fuskanta, kamar rashin tallafi daga gwamnati da kuma rashin kula da kayayyakin da aka samar a makarantu da al’ummomi, wanda ke kawo koma baya ga ayyukansu.

Ya kuma bukaci hadin kai daga masarauta da shugabannin al’umma domin gano wuraren da ke fama da matsalar ruwa, tare da kira ga jama’a su kula da kayayyakin da ake samar musu.

A nasa bangaren, Dan Makwayon Kano ya bayyana cewa fadarsa a shirye take wajen bayar da goyon baya da hadin kai domin magance matsalar ruwan sha.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin ƙungiyoyin, yana mai cewa irin wannan jajircewa na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma da kuma rage matsalolin da ke tattare da rashin ruwa mai tsafta.

By ukarofi