Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, da ɗansa Abdulaziz, inda ta cire zargin da ya shafi tallafawa ta’addanci kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A zaman kotu na ranar Laraba, lauyan Hukumar DSS, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an yi wannan gyara, tare da neman a maye gurbin tsohuwar ƙarar da sabuwa. Sabuwar tuhumar ta ta’allaka ne kan mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Lauyan waɗanda ake ƙara, Shaibu Aruwa, ya tabbatar da cewa an ba su sabuwar takardar ƙarar, kuma ya amince a karanta musu. Bayan an karanta, Malami da ɗansa sun musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince su ci gaba da kasancewa a kan belin da aka ba su tun ranar 27 ga Fabrairu.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranakun 26 ga Mayu da 15 ga Yuni domin ci gaba da shari’a.
A cikin sabuwar ƙarar, ana zargin an gano makamai da harsasai a gidan Malami da ke Birnin Kebbi.
Tun farko dai, DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa a ranar 3 ga Fabrairu bisa tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin tallafin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. A ranar 27 ga Fabrairu, kotu ta bada belinsu kan naira miliyan 200 kowannensu tare da sharuɗɗa.
