Haɗin kai da cigaban al’umma ne manufar Gwamna Yusuf — Hon. Bala Gwagwarwa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Manufar Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf na sanya ci gaban jihar a gaba abu ne mai matuƙar muhimmanci da zai haɗa kan ɓangarori daban-daban, musamman masu ruwa da tsaki kamar ‘yan siyasa, malamai, ‘yan kasuwa da sarakuna domin bunƙasa al’umma.

Tsohon zaɓaɓɓen shugaban tsohuwar ƙaramar hukumar Nasarawa, kuma tsohon kwamishina a Jihar Kano, tare da kasancewarsa tsohon ma’ajin jam’iyyar APC na ƙasa, Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce Jihar Kano na buƙatar samar wa al’ummarta, a ko’ina suke — ciki da wajen ƙasar nan — yanayin da zai sa kowa ya ji cewa yana da rawar da zai taka wajen ci gaban jihar. Ya ƙara da cewa, wajibi ne duk wani abu da za a yi a fara sanya buƙatar Kano a gaba domin ci gabanta da zaman lafiyarta.

Ya bayyana cewa idan aka aiwatar da wannan kyakkyawar manufa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ƙoƙarin ɗorawa, za a samu sauyi a yadda siyasar Kano ke gudana, sabanin yadda aka saba a baya ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata.

A cewarsa, a baya ana rarraba mutane bisa tsarin siyasa, inda ake ware su zuwa ɓangarori daban-daban, lamarin da ke hana haɗin kai da sanya Kano a gaba. Wannan, a cewarsa, ya janyo koma baya ga ci gaban jihar.

Ya ce Gwamnan Kano na ƙoƙarin sauya wannan tunani ta hanyar ɗora al’umma a kan turbar da za ta sa kowane ɗan Kano ya rika tunanin irin gudunmawar da zai bayar domin ci gaban jihar, yana mai jaddada cewa idan al’umma suka tsira, jihar ma za ta tsira.

Hon. Gwagwarwa ya ƙara da cewa, a kowane matsayi mutum yake — ko ɗan kasuwa ne, manomi, likita, ma’aikaci ko ɗan siyasa — ya kamata ya rika tambayar kansa irin gudunmawar da zai bayar domin ci gaban Kano.

Ya bayyana cewa, duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar APC, amma Gwamna Abba Kabir Yusuf yana ƙoƙarin wuce siyasa ta hanyar kira ga dukkan ‘yan Kano, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, su zo su ba da gudunmawa wajen gina jihar.

Ya ce wannan manufa ta “Kano a gaba” na buƙatar a rungume ta gaba ɗaya ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Kano, domin a dasa sabuwar akida a zukatan al’umma. Ya misalta hakan da tambarin Jihar Kano mai ɗauke da hoton raƙuma da dabino, wanda ke nuna tarihi da ƙwarewar Kanawa a kasuwanci da noma.

Hon. Gwagwarwa ya jaddada cewa duk inda ɗan Kano yake, idan ya ga tambarin Kano, ya kamata ya tuna da jiharsa, ba tare da danganta shi da jam’iyya ko wani mutum ba, domin manufar ita ce haɗa kai domin ci gaba.

Ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaba shi ne ɗaukar mulki a matsayin mallakin mutum ko ƙungiya, maimakon na al’umma baki ɗaya. Saboda haka, wannan gwamnati ta sanya Kano a matsayin alƙibla ta kowa.

Ya ƙara da cewa wannan tsari zai kawo bambanci da yadda a baya ake fifita ra’ayin wasu mutane ko ƙungiyoyi, wanda hakan ke hana wasu masu kishin Kano shiga cikin harkokin ci gabanta.

A ƙarshe, Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin sauya tunanin matasa, musamman wajen koyar da su su fifita gaskiya, ƙwazo da amana fiye da biyayya ga mutum ko jam’iyya.

Ya ce manufar ita ce a gina sabuwar al’umma mai haɗin kai, a kawar da ƙiyayya, tare da samar da hanyoyi masu yawa na haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.

By ukarofi