Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, ya shigar kan jagorancin David Mark a jam’iyyar.
A zaman kotun na ranar Talata, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayyana cewa “rashin ladabi na shari’a” ne a ci gaba da sauraron ƙarar a matakin kotun tarayya alhali akwai ɗaukaka ƙara da ke gaban kotun ƙoli.
Ya ƙara da cewa ƙarar da ke gaban kotun ƙoli na iya kawo ƙarshen batun gaba ɗaya, don haka ya zama dole a dakatar da ci gaba da shari’ar a kotun tarayya har sai kotun koli ta yanke hukunci.
A cikin ƙarar da aka shigar ranar 2 ga Satumba, 2025, Nafiu Bala ya lissafo jam’iyyar ADC, David Mark, Rauf Aregbesola (sakataren jam’iyya na kasa), Hukumar Zabe ta ƙasa (INEC), da Ralph Nwosu, wanda ya kafa jam’iyyar kuma tsohon shugaban jam’iyya, a matsayin wadanda ake tuhuma.
Nafiu Bala ya dage cewa bai taba yin murabus daga mukaminsa na mataimakin shugaban jam’iyya ba, don haka bisa tsarin jam’iyyar ya kamata shi ya karbi shugabanci bayan ficewar Nwosu. Daga bisani ya ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya, yana mai alƙawarin ƙalubalantar jagorancin Mark a kotu.
A cikin ƙarar, ya nemi kotu ta hana INEC amincewa da shugabancin David Mark, tare da tilasta hukumar ta ɗauke shi a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ADC.
Haka kuma ya shigar da wasu buƙatu na dakatar da jam’iyyar daga gudanar da tarurruka har sai an kammala shari’ar.
An fara sauraron buƙatarsa ta gaggawa a ranar 4 ga Satumba, 2025, inda mai shari’a ya umurci waɗanda ake tuhuma, ciki har da INEC, da su bayyana dalilin da zai hana a amince da buƙatar Nafiu Bala.
A zaman kotun na baya-bayan nan, mai shari’a Emeka Nwite ya ɗage shari’ar ba tare da ƙayyade lokaci ba, yana mai cewa zai zama “rashin ladabi na shari’a” a ci gaba da sauraron ƙarar a kotun tarayya alhali akwai daukaka kara da ke gaban kotun koli, wacce za ta iya kawo ƙarshen batun gaba ɗaya.
David Mark, shugaban ɓangaren ADC da ke rikici da Nafiu Bala, ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin wucin gadi da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke.
Sai dai a ranar 12 ga Maris, 2026, Kotun Daukaka ƙara ta yi watsi da ɗaukaka ƙararsa, tana mai cewa ba ta da tushe kuma ba ta da amfani.
Kotun ta umurci ɓangarorin da su koma kotun tarayya tare da ci gaba da kasancewa a matsayin da suke kafin rikicin har sai an yanke hukunci.
A ranar 1 ga Afrilu, Hukumar INEC ta sanar da cewa ba za ta kara hulda da ɓangaren ADC na Mark ko na Nafiu ba, bayan ta yi nazari kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara. INEC ta ce za ta guji hulɗa da kowanne ɓangare, ciki har da sa ido kan tarurrukansu.
Bayan wannan mataki na INEC, ɓangaren Mark ya daukaka kara zuwa Kotun Koli, inda ya ƙalubalanci hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
A ranar Talata, kwamitin alkalai biyar na Kotun ƙoli ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ya amince da a saurari karar cikin gaggawa.
