Yadda satar kayan tashoshin sadarwa ke durƙusar da kamfanoni – Bincike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fannin sadarwa na Nijeriya na fuskantar mummunar asara ta biliyoyin naira sakamakon ƙaruwa da satar muhimman kayayyakin aiki na tashoshin sadarwa, lamarin da ke barazana ga ɗorewar ingantaccen sadarwa a ƙasar.

Bayanan da Hukumar Kula da Sadarwa ta ƙasa (NCC), ta fitar sun nuna cewa a shekarar 2025 kaɗai an sace sama da kayayyaki 650 da suka haɗa da janareto, batirori da sauran muhimman na’urorin samar da wuta da ake amfani da su don samar da sabis mai kyau a tashoshin sadarwa.

Rahoton ya nuna cewa wannan matsala ta wuce matakin tangarɗar aiki kaɗai, inda ta zama barazana mai tsanani ga ginshiƙin sadarwar ƙasa, musamman ganin yadda kamfanoni ke dogaro da janareto da batir saboda ƙarancin wutar lantarki.

ƙungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Nijeriya, wato Association of Telecommunications Companies of Nigeria (ATCON), ta bayyana cewa matsalar ta kai matakin barazana ga wanzuwar fannin gaba ɗaya.

Shugaban ƙungiyar, Tony Emoekpere, ya ce kamfanoni yanzu sun koma yanayin kare kai fiye da faɗaɗa ayyuka, inda suke fi mai da hankali kan tsaron kayayyakinsu maimakon faɗaɗa sabis.

Ya bayyana cewa kamfanoni na amfani da sabbin matakai na tsaro, haɗin gwiwa da ƙungiyoyin sa-kai, ƙarfafa katangar tashoshi, da kuma amfani da fasahar sa ido daga nesa domin gano duk wani yunƙurin lalata kayayyaki a lokaci guda.

Haka kuma, ana sake tsara yadda ake gina tashoshin sadarwa domin rage yawan kayayyakin da ake iya sacewa cikin sauƙi, musamman batirori masu zaman kansu, duk da cewa har yanzu ana kai hari har kan sabbin tsarin hasken rana.

Masu ruwa da tsaki a fannin, ciki har da ATCON, ƙungiyar Masu Lasisin Sadarwa ta Nijeriya, Hukumar NCC da kuma NSCDC, na ƙara haɗa kai wajen musayar bayanan sirri da inganta hanyoyin daƙile laifuka.

Duk da waɗannan ƙoƙari, kamfanoni na ci gaba da fuskantar nauyi mai tsanani na kashe kuɗi wajen tsaron kayayyaki fiye da faɗaɗa hanyar sadarwa.

Emoekpere ya ce wannan yanayi ba zai ɗore ba, domin yana rage ƙarfin ci gaban fannin tare da ƙara tsadar aiki. Ya kuma bayyana cewa asarar da ake yi na kai wa biliyoyin naira a duk shekara, wanda daga ƙarshe ke shafar masu amfani da sabis ta hanyar raguwar inganci da ƙarin farashi.

Masana sun yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar na iya ci gaba da lalata tsarin sadarwa na ƙasa a daidai lokacin da ake ƙara dogaro da intanet da hanyoyin sadarwa a rayuwar yau da kullum.

By ukarofi