
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya koma jam’iyyar APC a hukumance bayan shafe makonni na shawarwari da kuma yawaitar jita-jitar sauya alƙiblar siyasarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Shekarau ya koma APC ne tare da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda shi ma jigo ne a PDP, lamarin da ke nuna an samu gagarumin sauyi a fagen siyasar Kano.
Sanannun ‘yan siyasar biyu sun sanar da haka ne a yau Lahadi a gidan Shekarau da aka fi sani da Fadar Munduɓawa a Kano, inda masu biyayya da magoya baya da dama suka halarta.
Da yake jawabi, tsohon gwamnan Kanon ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan shawarwari da nazari da ya yi game da zaɓin siyasa da yake da su, inda kuma baki ɗaya mahalarta taron suka yi masa mubayi’a bisa matakin nasa.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Shugaban APC na Ƙasa, Nentawe Yilwatda ya ziyarci Shekarau da Hayatu Gwarzo a gidan a wani yanayi na janyo ra’ayinsu shiga APC gabanin zaɓen 2027.
