
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta kama sama da waɗanda ake zargi da ta’addanci guda 20 a wani atisaye na musamman da jami’anta suka gudanar a sassan daban-daban na ƙasar yayin sabunta yaƙi da ta’addanci.
A cewar wani rahoton aiki da rundunar ta fitar a ranar Lahadi ga manema labarai a Abuja, an yi kamen ne yayin wani atisaye da ya ƙunshi dakarunta da sauran jami’an wasu hukumomin tsaro da kuma haɗin-gwiwar ƙungiyoyin ‘yan bijilante, inda suka hari maɓoyar ‘yan ta’adda da suka haɗa da masu garkuwa da mutane da masu aikata sauran manyan laifuka a jihohi da dama.
A Jihar Kogi, dakarun Birget ta 12 tare da haɗin gwiwar ’yan sanda da dakarun sa-kai, sun kamo mutane biyu da ake zargi da ta’addanci a ƙauyukansu na Kakuma Ileteju/Origa da Ijumu. An ƙwato babura da injinan sare itatuwa (chainsaw) a hannunsu.
Sai Jihar Sokoto, inda a nan ma sojoji sun share maɓoyar masu laifi a wasu al’ummomi, sannan sun ceto wani ɗan ƙasar Nijar da aka kwashe mako uku ana garkuwa da shi.
A Jihar Niger kuwa, rundunar ta lalata sansanonin ’yan ta’adda, ta kakkabe masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, sannan ta kama wasu da ake zargi.
Sai kuma Akwa Ibom, inda dakarun Birget ta 2 suka gano maɓoyar masu safarar miyagun ƙwayoyi, inda suka kama mutum shida tare da ƙwato Kilogiram 20 na wiwi (Cannabis), Codeine kwalba 15, Tiramadol, da sauran miyagun ƙwayoyi masu haɗari kamar Methamphetamine (Ice).
Haka kuma, an kuma samu tsabar kuɗi da adadinsa ya kai N431,500.
Sai kuma Jihar Ribas, inda dakarun suka lalata wuraren tatar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, sannan suka ƙwato bututu, tankuna da wasu kayayyakin tatar mai daga masu laifi.
Kazalika, a Filato an yi nasarar kama masu laifi tare da ƙwato makamai, harsasai, babura da kuma wasu maƙudan kuɗaɗe.
A ƙarshe, rundunar sojin ta ce an samu nasarorin ne sakamakon amfani da bayanan sirri da kuma kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban na ƙasa, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci a sassan ƙasar.
