Makarantu ba za su tafi hutun ƙarshen zango na biyu ba a Katsina – Sani Ɗanjuma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ba za a rufe makarantun firamare da na sakandire ba bayan kammala jarabawar zangon karatu na biyu (Second Term) da ɗalibai ke yi a halin yanzu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Malam Sani Ɗanjuma Suleiman, ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta yi kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su lura cewa, ɗalibai masu jeka-ka-dawo da kuma na makarantun kwana ba za su tafi hutun ƙarshen zangon karatu na biyu ba, saɓanin yadda aka saba yi a baya.

Ta kuma bayyana cewa bayan kammala jarabawar zangon na biyu za a ci gaba da zangon karatu na uku (Third Term) nan take ba tare da hutun ƙarshen zangon ba.

A cewar sanarwar, an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa an kammala dukkan darussa da aka tsara koyarwa ga ɗalibai kafin ƙarewar shekarar karatu ta 2025/2026.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin inganta harkokin ilimi a jihar.

By ukarofi