
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Lahadi aka yi jana’izar marigayi Ibrahim Galadima, tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa (NFF), a Masallacin Juma’a na Fagge da ke Kano.
Taron jana’izar ya samu halartar masu alfarma daga sassa daban-daban na Nijeriya.
Daga cikinsu akwai Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Alhaji Shehu Dikko, Shugaban NFF, Alhaji Ibrahim Musa Gusau da kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.

Tuni dai Ƙungiyar Maruwaita Labaran Wasanni ta Ƙasa (SWAN) ta aike da saƙon ta’aziyyarta ga iyalan marigayin bisa rasuwarsa bayan fama da wani rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Galadima, shi ne shugaban NFF, wato NFA a da daga shekarar 2002 zuwa 2006. Bayan haka ne ya miƙa ragamar jagorancin ga Alhaji Sani Lulu a 2006.
