
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Litinin ne wasu tsofaffin jami’an rundunar ’yan sanda da suka gudanar da zanga-zanga a yankin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sanya hannu akan fara amfani da dokar barin aiki na ‘yan sanda, wanda Majalisar Dattawa ta kammala aiki a kai tun a watan Disambar 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa, ƙudirin na neman fitar da rundunar ‘yan sanda daga tsarin fansho na ‘Contributory Pension Scheme’..
An ga yadda masu zanga-zangar ɗauke alluna masu rubutu suka tun daga yankin rassan gwamnati uku zuwa yankin hedikwatar hukumar.
Sun koka akan cewa an riga an cire sojoji, jami’an DSS, NIA, da sauran jami’an tsaro daga tsarin, amma an bar su a ciki duk da cewa su ne “uba” ga dukkan sauran hukumomin tsaron ƙasar.
Wani tsohon jami’i mai suna Nurudeen Dahiru ya bayyana cewa sun bauta wa ƙasa na shekaru 35, amma yanzu suna mutuwa cikin yunwa saboda ƙarancin fansho.
Haka ma wani Sufeto mai ritaya ya ce N24,000 ne kacal ake ba shi a wata, wanda ko abinci ba ya iya siya masa balle batun gina gida ko kula da iyali.
CSP Raphael Irowainu wanda shi ne Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, ya jaddada cewa babban burinsu shi ne shugaban ƙasa ya sa hannu kan dokar, wadda aka kai masa ofishinsa tun a ranar 16 ga Maris, 2026.
Wannan zanga-zanga na ɗaya daga cikin jerin bore da tsofaffin jami’an ke yi domin neman inganta rayuwarsu bayan barin aiki na tsawon da suka shafe wajen yi wa ƙasa hidima.
