
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Jihar Kwara sun halaka sojoji aƙalla guda uku a wani sabon hari da su ka kai da asubahin ranar Litinin a sansanin jami’an tsaro na haɗaka da ke kauyen Kemanji, a karamar hukumar Kaiama.
Rahotanni sun bayyana, cewa maharan sun kuma kwashe makamai da dama da wata motar yaƙi ta sojojin a yayin harin.
Mahara da dama ne suka shigo su ka far wa jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar uku tare da jikkata wasu jami’an, sannan su ka sace babura da alburusai mallakin jami’an.
Wani tsohon shugaban karamar hukuma da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar DailyTrust cewa maharan sun shigo ƙauyen da yawa tare da kai hari kai tsaye kan sansanin da ya kunshi sojoji, masu gadin dazuka da kuma ’yan banga.
Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti, yayin da wadanda suka fi muni aka tura su Ilorin domin samun kulawa ta musamman.
Majiyar ta ce duk da faruwar al’amarin, ba a kai wani hari ga fararen hula ba da ke yankin ba.
