Shari’ar Malami ta caɓe bayan kotu ta amshi hada-hadar biliyoyin Naira a matsayin shaida

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta amince da karɓar wasu muhimman shaidu guda tara da aka gabatar a gabanta a yayin cigaba da shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Abubakar Malami.

Ana zargin Malami ne da hannu a badaƙalar wanke kuɗaɗe da suka haura Naira biliyan 8.7.

Lauyoyin masu gabatar da ƙara sun miƙa waɗannan shaidu ne domin ƙarfafa hujjojin da suke gabatarwa a kansa.

Haka kuma, kotun ta bayyana cewa, shaidun sun cika dukkan ƙa’idojin doka da ake buƙata, don haka ta amince a karɓe su a matsayin hujja a shari’ar.

Ana sa ran wannan cigaba zai taimaka wajen hanzarta sauraron shari’ar, yayin da ake dakon karin bayanai daga ɓangarorin da abin ya shafa a zaman kotu na gaba.

Masana shari’a na cewa karɓar hujjoji daga kotu na nufin shari’ar na samun cikakken kulawa, wanda ya sa ake ganin akwai yiwuwar zurfafa bincike da ka iya tasiri ga hukuncin da za a yanke a nan gaba.

Mutane da dama na bibiyar wannan shari’a saboda muhimmancinta ga yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

By Babaji