Mahauta sun koka kan hauhawar farashin shanu a Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Mahauta ta Jihar Legas ta nuna damuwa kan yadda farashin shanu ke ci gaba da tashi, inda a halin yanzu ake sayar da saniya har zuwa Naira miliyan 2.5 — farashin da ya ma zarce na wasu tsofaffin motoci a kasuwa.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Bamidele Kazeem, ya bayyana haka ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi a Legas, inda ya danganta tashin farashin da matsalar tsaro, tsadar sufuri da kuma jinkirin aiwatar da shirin kiwon shanu na cikin gida.

A cewarsa, shanun da aka sayar da su kusan Naira miliyan 1.7 a shekarar 2025 yanzu sun kai tsakanin Naira miliyan 2.3 zuwa Naira miliyan 2.4, yayin da a wasu lokuta farashin ya haura zuwa Naira miliyan 2.5.

Ya ce, wannan tashin farashi ya jefa mahauta da masu saye cikin matsin lamba, inda da dama daga cikin ‘yan kasuwa ke fuskantar barazanar rufe sana’arsu.

“Motar da na saya a 2020 da Naira miliyan 2.1 yanzu ta fi arha idan aka kwatanta da farashin saniya. Wannan ya nuna yadda farashin ya yi tsanani,” inji shi.

Kazeem ya kuma bayyana cewa shanun da ake sayar da su a kan Naira miliyan ɗaya sun zama abin wuya a kasuwa, yana mai cewa matsalar da aka koka a kanta a baya ta yi ƙanƙanta idan aka kwatanta da halin da ake ciki yanzu.

Ya danganta wannan matsala da rashin tsaro da ke hana zirga-zirgar dabbobi cikin sauƙi a wasu sassan ƙasar, tare da hauhawar farashin man fetur wanda ya jefa kuɗin sufuri cikin tsadar gaske.

A cewarsa, yawancin shanun da ake sayarwa a Legas na fitowa ne daga arewacin Nijeriya, amma tsadar dizal da fetur ta sa jigilar su ta zama mai tsada sosai.

Haka kuma, ya bayyana cewa masu kiwon shanu na cikin gida ba sa iya biyan buƙata saboda rashin fara aiwatar da shirye-shiryen feedlot da ranching da gwamnatin jihar ta tsara.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta fara aiwatar da shirin Eko Ranching a Gbodu, Epe, yana mai cewa hakan zai ƙara samar da shanu a cikin gida, rage tsadar sufuri tare da saukaka farashin nama a kasuwa.

A cewarsa, shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga matasa da kuma taimakawa rage matsin tattalin arziki da ake fuskanta a fannin.

By ukarofi