Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Katsina ya amince da tsarin sulhu ko sasanci (Consensus) a zaɓukan fitar da gwani na ‘yan takarar jam’iyyar a zaɓukan shekarar 2027.
A lokacin zaman an kafa muhimman komitoci domin tabbatar da adalci da bin ƙa’ida, ciki har da kwamitin sulhu da sasanci wanda tsohon gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta, tare da tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema a matsayin mataimaki.
Hakanan an kafa kwamitocin sulhu a shiyyoyi 3 na jihar Katsina, yankin Katsina- Sanata Ibrahim Ida ne zai jagoranci kwamitin, sai yankin Funtua Hon. Tukur Ahmed Jiƙamshi zai jagoranta, shiyyar Daura kuwa tsohon ministan Gidaje Arc. Ahmed Musa Dangiwa zai jagoranchi na shiyyar Daura.
Sannan an kafa kwamitin tabbatarwa (Affirmation Committee).
A taron da ya gudana a gidan gwamnatin Katsina akwai gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa da mataimakin sa Farouk Lawal Joɓe da kuma tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema.
Akwai kuma ministocin gidaje da na al’adu, Injiniya Muttaƙa Rabe Darma da Hannatu Musa Musawa.
Sauran sun haɗa da manyan jami’an gwamnatin tarayya, yan majalisar dokokin ƙasa da na jiha.
Sai hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal da shugabannin ƙananan hukumomi 34 da ke jihar da sauran shugabannin jami’ya na ƙananan hukumomi.
